January 7, 2025

Jami’an tsaro sun ragargaza Lakurawa a jihar Kebbi.

Daga Sani Ibrahim Maitaya

Jami’an tsaro a jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, sun sami nasarar hallaka ƴan ta’addan Lakurawan da suka shiga bakin Garin Argungu su ka kora Shanu a daren jiya Alhamis.

Cikin wata sanarwa da mai ba wa gwamnan jihar shawara kan kafafen sada zumunta Aliyu Bandado ya fitar, ta ce Gwamnan jihar Kebbi bai taɓa yarda da yin wasa da sha’anin tsaron, al’ummar Kebbi da dukiyoyinsu ba.

Ƴansanda sun kama mutane 7 da ake zargin ƴan kungiyar asiri ne a Ogun.

Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.

Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane tare da ƙwato alburusai a Filato.

Sanarwar ta ce al’ummar ƙasar Argungu sun yi godiya ta musanman ga Gwamnan jihar, da jami’an tsaro a bisa ƙoƙarin fatattakar Lakurawan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *