Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria tare da hadin gwiwar UNICEF, za su dasa bishiyoyi har dubu biyu da tamanin a cikin watanni ukku don karfafa dorewar muhalli, da rage tasirin sauyin yanayi a yankin.
Shugaban jami’ar Farfesa Kabiru Bala ne ya bayyana hakan wani taron bita kan dasa bishiyoyi, sarrafa shara, da dabarun dorewar muhalli ga daliban ABU, wanda UNICEF ta shirya tare da hadin gwiwar jami’ar a Zaria.
Bala wanda Farfesa Sahalu Junaid ya wakilta ya bayyana cewa haɗin gwiwar na ƙunshe da shirin dasa bishiyoyi da sarrafa shara ta hanyoyin dorewa karkashin shirin Green Rising Initiative na UNICEF.
Ya ƙara da cewa Jami’ar ABU na da dadaddiyar al’adar dasa bishiyoyi, in da zuwa yanzu jami’ar ta dasa sama da bishiyoyi miliyan biyar a fadin harabar ta a cikin shekaru biyar da suka gabata.
A karkashin shirin sarrafa shara na wannan hadin gwiwa, UNICEF ta gina rumfunan zuba shara guda 12 a cikin harabar jami’ar domin sayen shara don sake amfani da ita.
Hukumar UNICEF da jami’ar ABU na son matasa su ɗauki waɗannan tsare-tsare a matsayin nasu, don su amfana da su a matsayin wata hanyar kasuwanci.
Shugaban jami’ar ya bayyana cewa za a dasa bishiyoyi 2,080 a fili mai girman hekta biyar, kuma UNICEF ta samar da tallafi ga masu aikin dasa bishiyoyin.
“Kowane mai aikin sa-kai a aikin dashen zai sami naira dubu biyu don sufuri da naira dubu daya da dari biyar don abinci; za mu fita filin dasa bishiyoyi akalla sau ukku a mako; a kowanne lokaci, za mu bukaci dalibbai 100,” in ji shi.
Ms. Theresa Pamma, kwararriya a fannin tsaftar ruwa da muhalli daga UNICEF Kaduna, ta ce hadin gwiwar da ABU na da matukar muhimmanci.
Pamma ta ce shirin Green Rising Project na UNICEF na da nufin karfafa matasa don su taka rawar gani a fannin dakile sauyin yanayi, kuma ABU na da dimbin dalibbai, hakan ya sa ta zama abokiyar huldar da ta dace.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.
-
Kswanaki biyu bayan rasa ran wasu mutum 16 a wani hatsarin mota a Abeokuta wasu ukun sun sake rasuwa in da wasu suka jikkata.