Kwamitin Gudanarwa na Kasa na jam’iyyar A. A ya yaba da hukuncin da Kotun sauraren kararrakin Zaben Gwamnan jihar Edo ta yanke, na ƙin amincewa da karar da wasu mambobin jam’iyyar karkashin jagorancin Adekunle Rufai Omoaje suka shigar, suna ƙalubalantar nasarar Gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shugaban jam’iyyar na ƙasa Chief Kenneth Udeze, ya jaddada cewa jam’iyyar A. A ko ɗan takarar ta na gwamna a jihar Edo ba su taba shigar da wata ƙara ba, da ke ƙalubalantar nasarar Okpebholo.
Jam’iyyar Action Alliance ta kara da cewa ƙarar da aka yi watsi da ita yunkuri ne na wasu mutanen da ba a san su ba, ƙarkashin jagorancin wani mai suna Adekunle Omoaje wanda ba ɗan takarar jam’iyyar ba ne, don bata sunan jam’iyyar.
Ya ce: “A ko da yaushe, Action Alliance ko dan takarar ta na gwamna a jihar Edo ba su taba shigar da wata ƙara ba da ke ƙalubalantar sakamakon zaben.”
Ya ce “Jam’iyyar ta yi mamakin rahoton da ke yawo a kafafen yaɗa labarai. A bayyana wa kowa cewa Adekunle Omoaje ya shigar da karar ne bisa raɓin kansa, yana ganin saka sunan jam’iyyar Action Alliance zai ba shi karfi.”
Udeze ya taya Okpebholo murna bisa nasarar da ya samu, tare da neman al’umma da su yi watsi da ƙarar da Adekunle Omoaje ya shigar, wanda ya ce jam’iyyar ba ta san shi ba.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa ɓangaren shari’a shi ne zuciyar adalci a cikin al’umma, kuma bazata yarda da shari’ar banza da sunan siyasa ba.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rasuwar Sheikh Idris: mun “fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki”- Gwamnan jihar Bauchi.
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Hukuncin kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen jihar Edo “babban kuskure ne da tauye adalci”-PDP