Jam’iyyar Social SDP a ranar Litinin ta bayyana cewa, ba za ta shiga kowace hadaka ba ko kuma bin dokokin hadaka kafin zaben 2027.
A cikin wata sanarwa da Sakatare na Kasa na jam’iyyar Olu Agunloye ya fitar, ya ce jam’iyyar ta fayyace cewa ba za ta bi kowane irin tsari ba.
Idan za’a iya tubawa a ranar Alhamis tsoffin ‘yan takarar shugaban kasa na 2023 Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na Labour Party, da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, sun sanar da yin wani kawance domin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Agunloye ya nuna takaicin sa kan yadda APC da PDP da suke mulkin Najeriya tun 1999, suka kasa sauke nauyin da ke kansu, yana mai jaddada cewa rashin adalci, cin hanci, sayen kuri’u, da rashin tsaro sun jefa kasar cikin matsin tattalin arziki, rashin aikin yi ga matasa, da talauci.
Ya bayyana cewa duba da wadannan matsaloli, kawo SDP a matsayin wata jam’iyya mai kishin ci gaba ya zama dole.
Ya ce, “Akwai kwararowar ‘yan siyasa iri-iri ciki har da manyan jiga-jigan siyasa zuwa SDP, kuma kowannen su yana da muradin sa, wanda hakan abu ne da za a iya fahimta.
Ya ce “Wasu sun zo ne don samar da hadin kai domin samar da ingantaccen shugabanci, wasu suna da niyyar karbe jam’iyyar da karfi, wasu kuma suna da burin tsayawa takara a 2027 a matakin jiha ko tarayya ko kuma su kasance cikin kokarin samar da wata sabuwar Najeriya, yayin da wasu suka shigo ne don biyan bukatun kansu ko daukar fansa ko kuma lalata jam’iyyar.
Ya kara da cewa “Yayin da muke karbar wadannan sababbin ‘yan jam’iyya, SDP za ta ci gaba da rike akalar jagoranci, zama mai gaskiya da adalci, da kuma jajircewa a kan ka’idojin adalcin zamantakewa.
“SDP za ta kasance mai adalci ga duk sababbin mambobi, kuma za ta samar da wurare idan bukata ta taso don ba su dama su kawo gudunmuwar su. Duk da haka, jam’iyyar ba za ta shiga wata hadaka ba, ko kuma a tilasta mata bin ka’idojin hadakar jam’iyyu.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙaramin Ministan Gidaje da Ci gaban Birane Yusuf Ata ya gargaɗi Kwankwaso kan batun jihar Rivers.
-
NNPP ta nesanta ta da Kwankwasiyya da su ƙungiyoyi ta na mai gargadin su dena bayyana kansu a matsayin cikakkun ƴaƴan jam’iyyar.
-
PDP ta sake dage taron Kwamitin Zartaswar ta na Kasa (NEC) zuwa ranar 15 ga watan Mayu.
-
Mijin Sanata Matasha ya buƙaci Akpabio da ya girmama matar sa.
-
Tinubu ya ya tabbatar da cewa tattalin arziƙin Najeriya ya na farfaɗo wa.