April 4, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Jiga-jigan ƴan siyasar jihar Katsina za su shiga ƙawancen Atiku don kayar da Tinubu a zaɓen 2027.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Katsina sun kuduri aniyar haɗa wani kawancen jam’iyyun adawa, domin kwace mulki daga jam’iyyar APC mai mulki a shekarar 2027.

Manyan jiga-jigan PDP a jihar karkashin jagorancin dakta Mustapha Inuwa, sun bayyana shirin su na shiga kawancen dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023 Atiku Abubakar, yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Katsina ranar Talata.

Inuwa wanda tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina ne, yayin jawabi ga mahalarta taron ya bayyana cewa, an kusa kammala tattaunawa don kafa kawance da nufin hambarar da APC a matakin jiha da kasa.

Ko da yake Inuwa bai bayyana kai tsaye cewa za su shiga kawancen Atiku ba, amma wasu majiyoyi masu tushe a cikin jam’iyyar, sun shaida wa jaridar THISDAY cewa an kammala shirin hadewa da jagoran su.

Ya ce: “Mun fara tattaunawa da mambobin jam’iyyar NNPP, PRP, da ma wasu jiga-jigan APC don kafa kawance gabanin zaben 2027″.

Ya kara da cewa “Wataƙila ya ba ku mamaki ku ji cewa wasu daga cikin mambobin jam’iyyar APC da ke mara wa wannan yunkuri baya suna rike da muƙamai masu muhimmanci, a gwamnatocin APC na jiha da na tarayya.”

Ya ce ƴaƴan wannan sabon yunƙurin adawa, wanda ya ƙunshi manyan ƴan siyasa daga ciki da wajen jihar Katsina, nan ba da jimawa ba za su cimma matsaya kan jam’iyyar da za su shiga, domin tunkarar zaben 2027.

Tsohon Sakataren Jam’iyyar PDP na ƙasa Sanata Umar Ibrahim Tsauri, da tsohon Sanata mai wakiltar yankin Daura Ahmed Babba Kaita, da Ahmed Musa Yar’Adua suna daga cikin jiga-jigan jam’iyyar da suka halarci taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *