Rundunar Sojin Sama ta Ƙasa (NAF) ta kashe ƴan ta’adda da dama a hare-haren sama da ta kai a jihar Zamfara.
Wani shafin yanar gizo mai suna Zagazola Makama, wanda ke kawo rahotanni kan yaki da ƴan ta’adda a yankin tafkin Chadi, ya bayyana cewa wani bangare na Operation Fansa Yanma ya kaddamar da hare-hare ta sama a maboyar ‘yan ta’adda inda aka nufi kai farmaki kan Yusuf Yellow, “shahararren shugaban ‘yan ta’adda,” a karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.
Jaridar TheCable ta rawaito Zagazola Makama na cewa wata babbar majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da cewa wannan farmakin da aka yi bisa bayanan sirri ya cimma gagarumar nasara.
Zagazola Makama ya ce an kitsa hare-haren ne da kyakkyawan shiri bisa dogaro da sahihan bayanan sirri.
“An aiwatar da aikin da cikakken tsari da kuma daidaito domin rage karfin ‘yan ta’adda,” majiyar ta tabbatar wa da Zagazola Makama.
Shafin ya kuma kara da cewa har yanzu ba a tabbatar ko Yusuf Yellow yana daga cikin wadanda suka mutu a farmakin ba.
“Yanzu haka jami’an tsaro na ci gaba da sintiri da kuma tattara bayanai domin tantance irin nasarar da aka samu,” shafin ya bayyana.
Sojojin Najeriya sun kara matsa kaimi wajen kai hare-haren sama da na kasa a karkashin Operation Fansa Yanma, domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An banka wa gidaje 24 da runbunan ajiyar hatsi wuta a jihar Jigawa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani.
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.