June 8, 2023

Kakakin Majalisar dokokin jihar Bauchi ya koma majalisa

Page Visited: 374
0 0
Read Time:42 Second

 

Hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi Rt. Hon. Abubakar Y Sulaiman a matsayin wanda ya lashe zaben Mazabar Ningi ta tsakiya a zaben daya gudana ranar Asabar.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Baturen zaben Prof. Shuaibu Muhammad yace Kakakin Majalisar na Jamiyyar PDP ya samu kuri’a 16,866 daya doke abokan karawar sa na APC Hon. Khalid Abdulmalik Ningi daya samu kuri’a 15,065 da Hon. Danlami Garba Bara’u na NNPP daya samu kuri’u 4,886.

Cikin jawabinsa na godiya bayan sanar da sakamakon Abubakar Sulaiman ya yi godiya wa Allah daya bashi wannan nasarar da jinjinawa al’ummar mazabar sa bisa zabar sa da suka sake yi.

Abubakar Y Sulaiman ya yi kira wa sauran abokan takarar sa dasu zo su hada hannu don ciyar da karamar hukumar Ningi gaba.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *