Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Kamfanin mai na Ƙasa, NNPCL, ya musanta dawo da tallafin mai a Najeriya, ya na mai cewa, bai biya kowa tallafin man fetur ba a cikin watanni tara da suka gabata.
Ranar Litinin ne wasu rahotanni suka yi ta ya wo a ƙasar, in da suka ambato shugaba Tinubu ya dawo da tallafi man fetur, wanda ya cire tun a ranar farko ta kama aikin sa a cikin shekarar 2023 a matsayin sabon shugaban ƙasar Najeriya.
Daily Nigerian ta rawaito cewa, Babban jami’in kula da harkokin kudi na kamfanin, Umar Ajiya a ranar Litinin ya ce NNPCL na kokarin cike gibin da ake samu na kudin shigo da man fetur ne kawai tsakanin kamfanin da gwamnatin tarayya.
“A cikin watanni takwas zuwa tara da suka gabata, NNPC Ltd., bai biya kowa ko kwabo a matsayin tallafi ba, babu wanda NNPCL ya biya kobo da sunan tallafi.
“Babu wani dan kasuwa da ya karbi kudi daga wajenmu da sunan tallafi.
“Abin da ke faruwa shi ne, muna shigo da ɗanyen mai, wanda ake kawo shi a kan wani farashi, kuma gwamnati ta ce mu sayar da shi a kan rabin farashin.
“Don haka bambancin farashin kawo ɗanyen man da rabin farashin shine abin da muke kira da gibi.
“Kuma yarjejeniyar tana tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kamfanin NNPC, domin a samu daidaito, wani lokacin su ba mu kudi, don haka babu wani kudi da za su yi musanyar hannu da wani dan kasuwa da sunan tallafi,” inji shi.
Ƴan Najeriya da dama sun shiga halin ƙaƙanikayi ne bayan cire tallafi man wanda ya haifar da tsadar rayuwa, abin ya kai ga ƴan ƙasar yin zanga-zangar lumana a kwanakin baya dan nuna damuwa kan halin matsi da ake ciki, suna masu nuna buƙatar a dawo da tallafin man, zanga-zangar da wasu sassan ƙasar ta juye zuwa tarzoma.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.