Daga Ummahani Ahmad Usman.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano a Arewacin Najeriya ta sanar da kama kwayar Tramadol da kudinsu ya kai Naira Miliyan Ashirin da Biyar.
A wata Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar dauke da sa hannuns, ta ce an kama Abba Musa, mai shekaru 30 mazaunin unguwar Rijiyar Zaki, a jihar Kano, yana tuka wata mota ƙirar Honda Accord wadda bayan bincike aka gano motar na ɗauke da fakiti dari biyar na Tramadol ɗin.
Bayan faɗaɗa bincike wanda ake zargin ya amsa cewa Motar ta abokinsa ce, Sulaiman Danwawu, mai shekaru 29, mazaunin unguwar Rijiyar Zaki, Sulaiman ya umarce shi da ya mika motar ga wani a unguwar ’Yan Kaba.
Kano: Ƴan Sanda Sun Cikawa Wani Mai Adaidaita Sahu Tankinsa Da Man Fetur Kyauta.
Kano: Ƴan Sanda Sun Cikawa Wani Mai Adaidaita Sahu Tankinsa Da Man Fetur Kyauta.
Wasu Daga Cikin Makarantun Da Muka Rufe Ba Su Da Mazauni Na Dindindin, -Gwamnatin Kano.
Rundunar ƴan sandan ta ce ta kama Sulaiman wanda ya amsa cewa, Motar tasa ce, kuma ya ɗauko Tramadol ɗin ce daga Onitsha jihar Anambra da nufin sayar da su a Kano.
Zuwa yanzu mataimakin kwamishinan ƴan sandan jihar Kano DCP Abubakar Zubairu, ya bayar da umarnin a mayar da waɗanda ake zargin sashin binciken manyan laifuka na rundunar, domin gudanar da bincike mai zurfi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Har yanzu ina matuƙar son Buhari, in ji fasinjan da ya kuɓuta daga hannun ƴan bindiga.
-
Kotu Ta Yi Fatali Da Buƙatar Abdujabbar Kan Neman Sauya Masa Kutu.
-
Kano: Matashiya Yar Shekara 16 Ta Rataye Kanta A Daki.
-
Sojojin Najeriya Na Farauta Waɗanda Suka Hausawa A Jihar Imo.
-
Gwamnan Kogi Ya Hana Sanya Takunkumin Rufe Fuska.