Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Jihohin Kano da Katsina, sun zama sahun gaba wajen matsalar rashin isassun takardun kudi a hannun mutane wanda hakan ya faro tun daga bankuna zuwa kan masu POS da ake samun kuɗi a wajen su.
Wani bincike ya nuna cewa a yanzu haka mafi yawancin jihohin Najeriya na fama da ƙarancin takardun kuɗi sai dai abun ya ta’azara a Kano da Katsina.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa bankuna ba sa bayar da tsabar kuɗin da ya wuce naira 20,000 ga mutum ɗaya a kowacce rana.
Matuƙa Adaidaita Sahu za su dawo biyan haraji a Kano.
Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano ta tseratar da ran mutum 4 a cikin watan Nuwamba 3 sun rasu.
Masu Garkuwa sun sace mutum 30 a jihar Katsina.
Yayin da masu Sana’ar POS ke cajar naira 200 akan kowacce dubu 10 da su ka ba wa mutum saɓanin naira 100 da su ka saba karɓa a baya.
Hakan ya fara yin tasiri ga masu ƙananan sana’o’i da kuma yankin karkara da wasu mutanen karkarar basa yin amfani da bankuna.
Wata matsalar bayan ƙarancin takardun kuɗi itace idan aka tashi tura kuɗi daga asusu zuwa wani asusun shima yakan bayar da da matsalar kuɗin yaki zuwa da wuri.
A makon daya gabata ne aka jiyo mataimakin shugaban Nigeria Kashim Shettima, na cewa bankuna su kawo ƙarshen matsalar ƙarancin tsabar Kudi a faɗin Najeriya.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.