August 8, 2022

Kano: Sinadari Mai Guda Ya Jawo An Kwantar Da Sama Da Mutum 200 A Asibiti.

Page Visited: 168
0 0
Read Time:44 Second

Rahotanni daga jihar Kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya na cewa an kwantar da mutane sama da mutane 200 a asibitoci daban-daban.

Lamarin ya faru ne biyo bayan da wasu Ƴan Jari Bola suka bude wata tukunyar gas mai dauke da wani sinadarin da ba a san ko menene ba a unguwar Sharada Ƴan Tagwaye a jihar.

Shugaban asibitin kwararru na Murtala Muhammad, Dr. Hussaini Muhammad ya bayyana cewa an kai mutane 60 asibitin kuma sun cigaba da karbar wasu.

A halin yanzu wadanda abin ya shafa suna sashen gaggawa na asibitin ana kula da lafiyarsu Sakamakon yadda Suka jikkata.

Har yanzu dai ba a gano sinadarin ba amma mutanen yankin sun bayyana cewa yana yaduwa a cikin iska, ya yi illa sosai ga mazauna yankin na unguwar Mundaɗu da makwaftan su.

Yayin da wasu da dama suke kwance a wasu asibitocin na daban.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *