September 22, 2021

Kano: Zargin Bata Sunan Ganduje Ya Jawo Jam’iyyar APC Ta Dakatar Da Dan Majalisar Tarayyar Najeriya.

Page Visited: 227
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 3 Second

Jam’iyyar APC reshan mazabar Sharada dake karamar hukumar birnin Kano ta sanar da dakatar da shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai, Sha’aban Ibrahim Sharada.

Cikin wata takardar sanarwar dakartawa mai dauke mai dauke sa hannun shugaban jam’iyyar mazabar Sharada, Abdullahi Umar ta bayani kan dalilin dakatar da dan majalisar.

“Biyo bayan shigar da korafin da magoya bayan jam`iyar APC mazauna mazabar Sharada su kai a ranar 8 ga watan June 2021, yanzu haka jam`iyar ta dau matakin dakatar da Sha`aban Sharada daga jam`iyar na tsawon shekara guda, tare da hana shi shiga sha`anin jam`iyar a kowanne mataki.

“Wannan matakin da jam`iyar ta dauka ya biyo bayan rahotan da kwamitin mutane bakwai da jam`iyar ta kafa ya mika a sati guda inda ya ce ya samu Sha`aban Sharada da laifin bata sunan gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, tare da shugabancin jam`iyar na mazabar tasa, da karamar hukuma da ma jihar baki daya.

“A cewar kwamitin wannan dabi`a ta Sha`aban ka iya kawo rashin jituwa da tashin hankali a jihar wanda hakan ya ci karo a manufar gwamnan na samar da zaman lafiya a jihar, tare da rushe darajar jam`iyar a idon magoya bayanta da al`ummar kasa.”

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us