December 2, 2021

Kasar Congo: Samada mutane 60 suka mutu sakamakon kifewar jirgin ruwa.

Page Visited: 148
0 0
Read Time:41 Second

Mahukunta a kasar jamhuriyar demokradiyar kongo sun bayyana cewa sama da mutane 60 ne suka rasa ransu yayin da jirgin ruwa ya kife dasu a kogin kongo.

 

An sami nasarar ceto mutane 300 yayin da wasu mutane 200 kuwa har yanzu babu labarin su.

 

Mazauna yankin da lamarin ya auku sun bayyana cewa jirgin ruwan yaci karo ne da dutse yayin da yake tafiya cikin dare wanda kuma hakan bai dace ba.

 

Ministan jin kai na kasar Steve Mbikayi ya bukaci a dauki mataki kan wadanda keda alhaki kan aukuwar hatsarin.

 

Jirgin dai yayi kazamar lodi ne inda ya debi pasinjoji 700, kafin aukuwar hatsarin inda mutane 60 suka rasa rayukan su, kana aka ceto mutane 300.

 

Ya jajanta wa iyalan mamatan inda ya bukaci daukan mataki kan hukumomin da abin ya shafa .

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *