Halima Abba Waziri.
A jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, tabon rikice-rikice da al’adu sun yi yawa sosai musamman a rayuwar mata da yara mata, cin zarafi ya na da nau’uka daban-daban, akwai rikicin cikin gida, auren dole, cin zarafi ta fuskar jima’i, da take muhimman hakkoki. Amma, duk da waɗannnan manyan ƙalubale, ana samun mutane masu juriya da jajircewa da kuma haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen dakile wannan matsala, sakamakon ƙoƙarin hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin addini, da sarakunan gargajiya.
Aisha Umar, ‘yar shekara 17 daga Potiskum, ta fuskanci mummunar kalubalen da ba zai iya misaltuwa ba. Aisha ta ba da labarin cewa, “Lokacin da mahaifina ya rasu a lokacin rikice rikice, an tilasta min auren wani dattijo mai yawan shekaru don biyan bashin da gidanmu suka ci. Bani da zaɓi, kuma bani da ta cewa.” Labarinta ya ƙara bayyana irin matsalolin da yara mata ke fuskanta a jihar Yobe, in da har yanzu auren dole ya zama ruwan dare, saboda al’ada da matsin tattalin arziki. Sai dai kuma ƙara wayar da kan jama’a da bayar da shawarwari na rage yawan matsalar sannu a hankali.
Gwamnatin Yobe ta ɗauki muhimman matakai na kare mata da yara mata daga wannan matsala. Ta hanyar amincewa da dokar yaƙi da cin zarafin jama’a, (VAPP), an aiwatar da dokoki don kiyaye waɗanda aka taɓa ci wa zarafi da hukunta masu cin zarafin. Hauwa Goni, Directa a ma’aikatar mata ta jihar Yobe, ta bayyana yadda gwamnati ke haɗa kai da ƙungiyoyi domin tallafawa waɗanda aka ci wa zarafi a ɓangaren shari’a, kula da lafiya da ba da shawarwari.
An kafa gida/cibiya ta musamman mai aminci tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin farar hula, don zama mafaka ga mata sama da 150 don kaucewa cin zarafi.
Ban taɓa tunanin zan tsira ba,” in ji Fatima, ‘yar shekara 19 da ta tsira daga rikicin cikin gida. “Cibiyar ta bani damar sake gina rayuwata da kuma yin hulɗa da mutanen da suka fahimci halin da nake ciki”.
A wannan yanki da addinin musulunci ke da tasiri sosai, malaman addinai sun zama ƙashin bayan magance waɗannnan matsaloli masu cutarwa. Sheikh Musa Ali, fitaccen malamin addini a Damaturu, ya yi suna sosai wajen yin wa’azi kan bukatar kare hakkin mata. “Musulunci bai yarda da auren dole ko cin zarafi ba,” kamar yadda ya jaddada a ya yin wani taron wayar da kan jama’a.
Halima, wacce ta kasance ɗaya daga cikin mahalarta shirye-shiryen wayar da kan al’umma ƙarƙashin jagorancin kungiyar mata Musulmi ta Jihar Yobe, ta yarda cewa tunaninta ya canza. “Kafin wannan shirin, na yi tunanin cewa ba laifi ba ne miji ya yi wa matarsa dukan tsiya. Amma, yanzu na fahimci cewa cin zarafi ba ya cikin addininmu.”
Su ma sarakunan gargajiya sun tashi tsaye wajen sauya wannan mummunan lamari. Mai martaba Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Suleiman, na cikin masu jan hankali game da muhimmancin ilimin ‘ya’ya mata da kuma kawar da al’adar aurar da kananan yara. Shawarwari da hoɓɓasarsa ya zaburar da sarakunan yankin, inda suka ɓullo da dokokin da suka haramta muggan al’adu da sauran munanan abubuwan da ke cutarwa.
“Al’ummarmu ba za su iya ci gaba ba idan har muka ci gaba da hana ‘ya’yanmu mata ’yancin samun ilimi da ’yancin fadin albarkacin baki,” in ji shi a wani taron jama’a a Gashua. Waɗannan matakai da ke samun goyon baya da tallafin kungiyoyi irin su UNICEF da Plan International, sun fara canza halayen al’umma.
Ƙungiyoyin fararen hula sun taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa waɗanda suka fuskanci matsalar cin zarafi da kuma wayar da kai. Wata ƙungiyar ba da tallafi mai suna The Portrait of Lake Child Initiative (PLCI) ta samar da shirye shiryen koyar da sana’oin hannu da ba da shawarwari kan harkokin zamantakewa don taimakawa mata su sake gina rayuwarsu. Zara, ‘yar shekara 25, wadda ta taɓa fuskantar matsalar cin zarafi, ta sami mafita da sauyin rayuwa ta hanyar ɗaya daga cikin shirye-shiryensu na ɗinki. “Lokacin da na tsere wa mijina da ke cin zarafi na, bani da komai. Amma ta hanyar PLCI, na koyi sana’a kuma yanzu zan iya ciyar da kaina da ‘ya’yana,” in ji ta.
Kungiyar mata ta ƙasa (NCWS) a Yobe ta ba da agaji ta ɓangaren shari’a ga waɗanda aka ci wa zarafi, tare da tabbatar da hatta matan da aka mayar da su saniyar ware sun sami adalci. “Mun ga ƙaruwar yawan mata masu son bayar da rahoton cin zarafi,” in ji Hajiya Fatima, ko’odinetan NCWS ta jihar. “Manufarmu ita ce mu tabbatar da kowace mace ta san ‘yancinta kuma tana da hanyoyin aiwatar da su.”
Amina, ‘yar shekaru 22 daga Geidam, ta bayyana yadda ta sami damar bayyana halin da take ciki, bayan shiru na shekaru. “An yi min aure ina da shekara 16 kuma na sha fama da cin zarafi na tsawon shekaru. Amma bayan halartar wani taron bita, na samu kwarin gwiwar barin wannan gida da ake cin zarafina. A yau ina gudanar da wata ‘yar ƙaramar sana’a, kuma na kuɗiri aniyar taimakawa wasu mata su sami karfin gwiwa”.
A Potiskum, ba’a bar samari a baya ba, inda suma suka shiga sahun masu yaki da cin zarafi. Wata ƙungiyar da matasa ke jagoranta, mai suna ‘Boys for Change’, suna tattaunawa da takwarorinsu game da mutunta mata da mu’amalantarsu ta hanyar da ta da ce. “Cin zarafi ba alamar karfi ba ne,” in ji Musa, ɗaya daga cikin ‘yan kungiyar.
Duk da ci gaban da aka samu, akwai kuma ƙalubale. Waɗanda suka tsira daga matsalar cin zarafi sukan fuskanci ƙyama da tsangwama, wanda ke hana su neman taimako ko tallafi. Ƙarancin kuɗi da kayan aiki yasa ba a iya samun damar shiga yankunan karkara masu nisa sosai, sannan har yanzu akwai matsala ta fuskar al’adu. “Muna buƙatar ƙarin zuba jari a fannin ilimi da ababen more rayuwa,” in ji Hauwa Goni. “Ta hanyar magance tushen cin zarafi – talauci, jahilci, da al’adu masu cutarwa ne kaɗai za mu iya samar da sauyi mai ɗorewa.”
Ga waɗanda suka taɓa fuskantar cin zarafi kamar Aisha, Fatima, da Zara, ƙarfin hali, juriya da juriyarsu sun zame musu ƙashin bayan samun nasara. Labarinsu na tunatar da mu cewa canji yana yiwuwa idan ɗaiɗaikun mutane da al’umma sun haɗa kai. “Sauyi ba ya yiwu wa dare ɗaya,” in ji Sheikh Musa. “Amma duk wani mataki na gaba, duk wata rayuwa da aka ceto, nasara ce.”
A wata tattaunawa da aka yi kwanan nan, DSP Fati Adamu ta jaddada cikakken kudirin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya na kare mata da ‘yan mata daga duk wani nau’in tashin hankali da cin zarafi.
Ta bayyana a fili cewa ‘yan sanda suna matuƙar Allah wadai da duk wani nau’in cin zarafi da ya shafi bambancin jinsi (GBV), wanda ya haɗa da cin zarafin mata a gida, cin zarafi ta hanyar jima’i, duka, da sauran nau’ukan cin zarafi. DSP Adamu ta tabbatar wa al’umma cewa duk wanda aka samu da aikata irin waɗannan laifuka za a hukunta shi bisa ƙa’idar doka.
Ta kuma bayyana matakan da rundunar ‘yan sandan ke ɗauka don magance GBV, ciki har da wayar da kan jama’a, gudanar da tarukan ilimantarwa, da haɗin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da adalci ga waɗanda suka tsira daga irin wannan cin zarafin.
DSP Fati Adamu ta yi kira ga al’ummomi su taka rawar gani wajen bayar da rahoton duk wani laifi ko cin zarafi, tana kuma ƙarfafa jama’a su ɗauki ‘yan sanda a matsayin abokan haɗin gwiwa a yaƙin da ake yi da GBV.
Wannan bayanin ya nuna yadda rundunar ‘yan sanda ta fahimci matsalar cin zarafi ga mata da ‘yan mata a Najeriya da tasirinsa ga waɗanda abin ya shafa, iyalansu, da al’umma baki ɗaya.
Ta hanyar alkawarin bin doka da ƙirƙirar muhalli mai aminci ga mata da ‘yan mata, Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya na nufin gina al’adar ɗaukar alhaki da tabbatar da adalci ga duk waɗanda suka tsira daga GBV.
Yayin da Yobe ke ci gaba da fafutukar kawo karshen cin zarafin mata da yara mata, sakon a bayyane yake cewa: babu wata mace ko yarinya da ya kamata ta sha wahala cikin shiru. Ta hanyar juriya da jajircewa, makoma mafi aminci da daidaito na gab da tabbata.