March 12, 2025

Kotu a Kaduna ta yanke hukuncin datse wa wasu maza biyu mazakuta da kuma rataya.

Mutum biyu da aka bayyana sunayen su da John Moses da Yakubu Mohammed, an yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya da kuma yanke azzakari a Jihar Kaduna.

An yanke wa Moses hukunci ne bisa laifin fyade da zina da dangi (incest), yayin da aka samu Mohammed da laifin fyade.

Leadership ta rawaito, an gurfanar da su ne bisa dokar Sashe na 258 (1) na Kundin Hukunta Manyan Laifukka na 2017 wanda aka yiwa gyaran fuska.

Haka nan kuma, wani mutum mai suna Mustapha Musa an yanke masa hukuncin daurin rai da rai bisa laifin fyade karkashin wannan doka.

Dukkan su su ukun sun fuskanci tuhumar da Gwamnatin Jihar Kaduna ta shigar a kan su daban-daban.

Kwamishinar Ma’aikatar Kula da Harkokin Bil Adama da Ci gaban Jama’a ta Jihar Kaduna Hajiya Rabi Salisu, ita ce ta bayyana wannan ci gaba a Kaduna ranar Laraba.

A cewar ta, ma’aikatar ta samu nasarar hukunta wadannan mutane ukku tsakanin watan Yuni 2024 da watan Fabrairu 2025, tare da nuna cewa hukuncin zai zama izina ga masu aikata irin wannan mugun aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *