Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Wata Kotu a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, ta ba da umarnin a tsare mata wani Ɗan Jarida da aka gurfanar a gabanta kan zargin ɓatancin ga gwamna Abba Kabir Yusuf.
Tin da farko Ƴansanda ne suka fara tsare matashin Ɗan Jaridar mai suna Muktar Dahiru kafin daga bisani su gurfanar da shi a gaban kotun.
Ana zargin Ɗan jaridar wanda ke aiki a gidan rediyon Nijeriya Pyramid FM Kano, ne da yaɗa wani labari na zargin Gwamna Abba Yusuf, kamar yadda DCL Hausa ta rawaito.
An kuma zarge shi da sakin wata hirar sauti da wani dan siyasa a bangaren adawa ya zargi gwamnan da cin hanci da rashawa.
An gurfanar da Dahiru a gaban Kotun Majistare ta 24 da ke Gyadi Gyadi a birnin Kano.
A makon da za mu shiga ne za a koma zaman kotun domin ci gaba da sauraron ƙarar.