June 8, 2023

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Kotu Ta Aike Da Ɓarawon Da Ya Yiwa Ɓarawo Sata Gidan Gyaran Hali.

Page Visited: 1413
0 1
Read Time:2 Minute, 0 Second

Daga Fa’izu Muhammad Magaji

Wata kutun shari`ar musulinci mai lamba biyu da ke zaune Tashar Babiye ta aike da wasu barayi biyu gidan yari bayan samun su da laifin zata.

Tin da farko a cewar `dan sanda mai gabatar da `kara Sajan Yahuza Mohammmad, a ranar 6 ga watan Agusta na shekarar 2022 da misalin karfe 8 na safe, wani mai suna Yakubu Mai Soda, `dan shekara 20, mazaunin unguwar Doya a cikin garin Bauchin jihar Bauchi, ya je `Yan Doya da ke kasuwar Muda Lawan, ya tattare wayoyin hannu `kirar Tecno spack 4, guda uku, Itel guda 1, Hula Zanna guda 5, da kuma takalmi guda 1, a cikin wani shago a kasuwar.

`Dan sandan ya cigaba da cewa jummular kimanin kudin wayoyin sun kai 74,000 , acewarsa wayoyin mallakin wasu mutane biyu, Kudin huluna sun kai naira dubu 25.

Dan sandan ya kuma ce, an kama barawo na biyu Sunusi Abdullahi, mai shekara 25, da ke da zama a unguwar Sarakuna, ne lokacin da aka kama barawo na farko ana tsaka dukansa wanda barawo na biyu ke cikin masu dukan barawo na farkon.

Ana cikin dukan barawo na farkone kwatsam sai barawo na biyu ya zare daya daga cikin wayoyin da barawon farko ya sata kirar Itel a aljihunsa.

Sajan Yahuza, ya kara da cewar sun kira masu kayan suna tambayarsu, akan kowa ya fadin lambarsa, a kira don abawa masu kaya kayansu, ana kiran waya, kawai sai akaji waya tayi kara a aljihun barawo na biyu, inda shima aka cika hunnu dashi.

Wanda aikata hakan laifine da ya saba wa kundin laifuffuka sashi na 150 ta tsarin dokar Penel Code.

Bayan karanta wa wa`danda ake zargi tuhume-tuhumen da ake musu sun amsa laifinsu.

Kotu Ta Yi Fatali Da Buƙatar Abdujabbar Kan Neman Sauya Masa Kutu.

Kotu Ta Aike Da Tsohon Babban Akanta Janar Ahmed Idris Da Mutum Biyu Gidan Yarin Kuje.

Kotu Ta Aike Da Tsohon Babban Akanta Janar Ahmed Idris Da Mutum Biyu Gidan Yarin Kuje.

Alkalin kotun Barrister Muktar Adamu Bello Dambam, ya yanke ma barawon da ya yi sata ga barawo hukumcin zaman Shekara 1 a gidan Dan Kande, ko biyan tara Naira dubu 15, tare da bulala 10 a gaban kotu.

Inda kuma alkalin ya yanke wa barawon farko daurin Shekara 1 a gidan Dan kande, ko biyan tara Naira dubu 20, tare da bulala 10 a gaban kotu.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *