Kotu Ta Aike Da Matashi Gidan Yari Saboda Satar Goyon Masara 22.

Page Visited: 622
0 0
Read Time:1 Minute, 18 Second

Daga Fa’izu Muhammad Magaji

Alkalin kotun shari’ar Muslunci mai lamba 2 da ke zaune a Tashar Babiye a jihar Bauchi Barrister Muktar Adamu Bello Dambam, ya yanke wa wani matashi mai suna Attahiru Dahiru, ɗan shekara 20, mazaunin unguwar a New GRA a garin Bauchi, hukumcin ɗaurin watanni 8 a gidan gyaran hali da tarbiya, ko kuma zaɓin biyan tara ta Naira dubu 10, tare da bulala 10 a gaban kotun.

Hukuncin ya biyo bayan samun matashin da laifin shiga gonar wani mutum mai suna  Adamu Abdullahi, inda suka balle masa goyon Masara har guda 22 tare da wani  mai suna Hamza wanda ya gudu.

Tinda farko rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ce ta gurfanar da  Attahiru gaban kotun,  bayan wanda suka shigarwa gonar ya shigar da korafi ga rundunar a kansu, wanda mai gonar ya ce daman an sha shiga gonar tasa ana yi masa barna.

Wakilinmu Fa’izu Muhammad Magaji, ya rawaito cewa ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya faɗawa kotun cewa idan aka samu mutum da aikata hakan, laifine da ya saɓa wa kundin laifuffuka da hukunce-hukunce sashi 125,183,150, na tsarin dokar penel code.

Kotu Ta Ci Abduljabbar Tarar Naira Miliyan 10.

Kano: Kotu Ta Nemi Rundunar Ƴan Sanda Ta Binciki Safara’u, Ado Gwanja, Mr.422, Ɗan Maraya, Murja Ibrahim.

Bauchi: Wata Kotu Ta Aike Da Wasu Matasa Gidan Gyaran Hali, Bayan Samun Su Da Laifin Tayar Da Hankalin Al’umma.

Bayan karanta ma wanda ske zargi laifinsa, nan take  ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, hakan yasa aƙalin yanke masa hukumcin.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Matashi Ya Yiwa Mahaifin Budurwarsa Mummunan Rauni Bayan Ya Hana Shi Kaiwa Dare Idan Yaje Zance.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Saurayin ya yiwa mahaifin budurwarsa rauni ne bayan da baban budurwar tasa ya hana shi kaiwa dare idan yaje zance a garin Ɗan Hassan, da ke ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano da ke arewacin Najeriya. Arewa Radio ta rawaito cewa, an jiwa mahaifin budurwar raunine bayan da ya umarce saurayin […]

Read More
Labarai

Sojoji sun sake yin juyin mulki a kasar Burkina Faso.

Sojoji a Burkina Faso sun hamɓarar da shugaban gwamnatin sojan ƙasar, Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a yau Juma’a, bayan ya hau mulki a watan Janairun da ya gabata. Wata sanarwa da sojojin suka karanta ta kafar talabijin ɗin ƙasar ta ce an rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa daga daren yau. Haka nan sun […]

Read More
Labarai

Lauyan Gwamnatin Kano Ya Nemi Kotu Ta Yiwa Abduljabbar Hukunci.

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake Kofar Kudu Karkashin me Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta ce za ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci kan karar da Gwamnatin Jahar Kano ta shigar da Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara bisa zarginsa da kalaman batanci. Yayin zaman na Yau dukkannin bangarorin Shari’ar sun gabatar da Jawabansu na karshe […]

Read More