Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya musanta zarge-zargen da hukumar EFCC ke yi masa guda 16 bayan an gurfanar da shi gaban kotu a Abuja a yau Laraba.
EFCC ta gurfanar da Bello bisa zargin laifuka 16 da suka hada da karkatar da kudade da su ka kai Naira biliyan 110.
Sauran wadanda ake tuhuma tare da Bello sun hada da Umar Shoaib Oricha da Abdulsalami Hudu, wadanda su ma su ka musanta -tuhumen.
EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello a Kotu kan almundahana da naira biliyan 110.
An tsagaita bude wuta a Lebanon bayan cimma yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Hesbollah.
Ƴarsanda ta yi barazanar kashe kanta da ƴaƴanta.
Joseph Daudu, lauyan Bello, ya miƙa rokon neman ba da belin wanda ya ke karewa, amma sai lauyan EFCC Kemi Pinheiro ya soki rokon.
Daga ƙarshe Kotun ta ba da umarnin ci gaba da tsare Yahaya Bello har sai 10 ga watan Disamba, in da za koma domin ci gaba da sauraron ƙarar.
A ranar Alhamis ne hukumar ta tabbatar da kama Yahaya Bello wanda ta ce ta tsare shi, an jima ana wasan ɓuya tsakanin sa da hukumar wadda take neman sa ruwa a jallo tun a watan Afrilun 2024.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.