Babbar Kotun Jihar Abia da ke zamanta a Obehie karamar hukumar Ukwa ta yamma ƙarƙashin mai shari’a L.T.C. Eruba, ta dakatar da aiwatar da dakatarwar da aka yi wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma Shugaban Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP, Adolphus Wabara.
A cikin umarnin kotu da aka samu a ranar Assabar, kotun a wata doka da ta sanya wa hannu a ranar 25 ga watan Fabrairu 2025, ta hana shugabancin jam’iyyar PDP na jihar Abia, ƙarƙashin jagorancin Abraham Amah aiwatar da dakatarwar.
Wabara a cikin ƙarar da ya shigar mai lamba HUK/8/2025, ya kai Amah kotu yana neman a hana shi aiwatar da dakatarwar da aka masa.
Bayan sauraron ƙorafin Wabara, kotun ta bayar da umarni cewa: “An hana wanda ake ƙara aiwatar da dakatarwar da aka yi wa mai ƙara/dauke da ƙarar daga jam’iyyar PDP ko yin wani abu da zai shafi matsayin sa, a matsayin Shugaban Kwamitin Amintattun PDP har sai an yanke hukunci kan takardar buƙatar da ke gaban kotu.”