Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Babbar kotun johar Kano, mai namba 11, ƙarkashin jagorancin Mai Justice Nasir Saminu, ta sallami wata dattijuwa mai suna A’isha Hashim, mazauniyar garin Daƙasoye da ke ƙaramar hukumar Bebeji, wadda aka gabatar mata bisa zargin ta kashe wata ƙaramar yarinya mai shekaru 2 da kuma jefa gawarta a Rijiya.
Tun a ranar 22 ga watan Augustan 2022, aka zargi dattijuwar da kashe yarinyar mai suna Maryam, In da jami’an Ƴansanda su ka kama ta don gudanar da bincike, daga bisani kuma suka gurfanar da ita a gaban kotu.
Lauyan Gwamnatin jahar Kano, Barista Zaharaddin Mustapha, ya gabatar da shaidunsu, ya yin da wadda ake zargin ta kare kanta.
Kotu: An Tsare Ɗan Jarida A Gidan Yari Kan Zargin Ɓata Sunan Gwamnan Kano Abba.
Kotu Ta Tisa Kyeyar Uba Da Ɗansa Gidan Kaso Kan Zargin Kashe Limami A Kano.
Alkalin kotun justice Nasir Saminu, ya ce shaidun da aka gabatar ba su tsaya ba, don haka ya wanke dattijuwar daga zargin.
Lauyan Dattijuwar , ya bayyana gamsuwarsa da hukuncin kotun, har ya tabbatar da cewar daman shaidun da lauyoyin Gwamnatin su ka gabatar, su da kansu sun ce, ba Ido da Ido suka ga dattijuwar ba.
A nata ɓangaren wadda kotun ta sallama ta ce kotun ta yi mata adalci domin a lokacin da lamarin ya faru ta na Gona.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.