January 31, 2023

Kotu Ta Yanke Wa Wani Matashi Daurin Rai Da Rai Bayan Samun Sansa Da Aikata Fashi Da Makamin Babur Mai Kafa Biyu.

Page Visited: 126
0 0
Read Time:58 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Wata babbar kotun jihar Bauchi mai lamba biyar a karkashin jagorancin mai shari`a Mu`azu Abubakar, ta yanke wa wani matashi mai suna Umar Hardo, mazaunin unguwar Sarakuna a birnin Bauchi, hukuncin zaman gidan gyaran hali na dindindin, sakamakon samunsa da laifin yin fashi da makami.

Ti nda farko dai gwamnatin jihar Bauchi ce ta yi karar matashin gaban kotun ta hannun ma`aikatar shari`a ta jihar Bauchi, bisa tuhume-tuhume guda biyu.

Yin fashin babur a hanyar zuwa Dass ga wani mai suna Idris Abdullahi, mazaunin hanyar Gombe, ta hanayar amfani da bindiga kirar hannu da kuma rike makami da harsashai guda uku kirar gida, a ranar biyar ga watan shidan shekarar 2021, wanda aikata hakan laifi ne da ya saba da kashi daya biyu cikin baka da kashi biyu na hukuncin rike makami ba tare da izini ba, da kuma sabawa sashi na kashi uku daya cikin baka.

Alkalin kotun mai shari`a Mu`azu Abubakar ya yanke masa hukuncinne bayan saurarar shedun masu kara.

Sai dai kuma har zuwa lokacin hada wannan labarin matashin bai daukaka kara ba kamar yadda doka ta bashi dama,

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *