Kotu Ta Yi Fatali Da Buƙatar Abdujabbar Kan Neman Sauya Masa Kutu.

Page Visited: 1611
0 0
Read Time:31 Second

Kotun shari’ar musulunci da ke kofar Kudu a jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, ta yi fatali da buƙatar da Sheik Abduljabbar Kabara ya mika mata ta bakin lauyansa, Barista Dalhatu Shehu, na neman a dauke shari’ar zuwa wata kotu.

Abdujabbar dai ya yi zargin Alkali ya yiwa shari’ar zagon kasa wanda ke ganin kotun ba zata yi masa adalci ba.

Wata Kotu A Kano Ta Sake Hana Belin Sheikh Abduljabbar.

Gwamnatin jihar Kano dai na zargin Malamin da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammadu S A W, da kuma tada hankalin al’ummar jihar Kano, wanda malamin ke musanta hakan.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Tsaro

Mayakan ISWAP sun hallaka jami’an tsaro da farar-hula a Borno.

Mayakan jihadi sun kai hari sansanin soji da wani yankin Borno tare da kashe sojoji 9, da ‘yan sanda biyu da kuma farar-hula, kamar yada majiyoyin tsaro da mazauna yanki suka tabbatar. Mayakan IS sun farwa garin Malam Fatori, a ranakun daren Juma’a da kuma safiyar Asabar, a cewar majiyoyin. A cewar bayanan da aka […]

Read More
Tsaro

Kano: Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Jawo Rasa Ran Mutum Guda Da Jikkata Wasu Biyar – Ƴan Sanda.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rundunar ƴan sandan jihar Kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya, ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya inda kuma biyar suka jikkata sakamakon rikicin Manoma Da Makiyaya da ya afku a garin Kuka Bakwai, da ke ƙaramar hukumar Minjibir a jihar. Rundunar yan sandan ta ce an samu ɓarkewar  rikicin ne […]

Read More
Tsaro

Masu Garkuwa Sun Bukaci A Basu Kudin Fansa Har Naira Miliyan 250 A Katsina Bayan Sun Sace Mutum 43.

Daga Suleman Ibrahim Maddibo wasu bayanai daga jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya na cewa, al’ummar kauyen Bakiyawa da ke yankin Batagarawa na cikin firgici bayan da ‘yan ta’addan da suka sace mazauna kauyen 43 suka bukaci da a biya su naira miliyan 250 a matsayin kudin fansa, kafin sako mutanen da suke […]

Read More