April 1, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Kotun Ƙoli ta raba gardama kan rikicin Sakataren jam’iyyar PDP na tarayyar Najeriya.

Kotun Koli ta ayyana Samuel Anyanwu na hannun daman Ministan Babban Birnin Tarayya, a matsayin Sakataren jam’iyyar PDP na kasa.

Anyanwu da Sunday Ude-Okoye sun kasance cikin takaddama mai tsanani kan wannan matsayin, lamarin da ya haddasa rabuwar kai tsakanin jiga-jigan jam’iyyar.

Duk da haka Ude-Okoye ya samu goyon baya daga bangarori daban-daban na jam’iyyar, wadanda suka dogara da hukuncin wata Kotun Daukaka Kara da ke zaman ta a Enugu.

Wannan Kotun Daukaka Karar ta tabbatar da korar Anyanwu da wata Babbar Kotun Tarayya da ke Enugu ta yi.

Sai dai a wani hukunci na hadin gwiwa da aka yanke a ranar Juma’a, kwamitin alkalai biyar na Kotun Koli ya bayyana cewa batutuwan da suka shafi shugabanci ko zama mamban jam’iyya lamari ne na cikin gida, don haka bai kamata a kai shi kotu ba.

A cikin hukuncin da Mai Shari’a Jamilu Tukur ya karanta, Kotun Koli ta ce babu wasu dalilai na musamman da za su ba kotu hurumin yanke hukunci kan lamurran cikin gida na wata jam’iyya.

Wadannan dalilai na musamman kamar yadda kotun ta bayyana su ne: idan Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba kotu irin wannan hurumi, ko kuma idan an aikata wani laifi ko karya alkawari.

Neman matsayin Sakataren jam’iyyar na Kasa ya zama abin takaddama, tun bayan da Anyanwu ya bar shi domin tsayawa takarar gwamnan Jihar Imo inda ya sha kaye.

Bayan faduwar shi zaben, kokarin sa na dawo wa kujerar sakataren ya jefa jam’iyyar cikin rikici.

Wata Kotun Daukaka Kara da ke zaman ta a Enugu ta tabbatar da hukuncin da wata Babbar Kotu ta yanke a ranar 20 ga watan Disamba 2024, na tsige Sanata Anyanwu a matsayin Sakataren PDP na Kasa tare da tabbatar da Ude-Okoye a matsayin sahihin sakatare.

Sai dai, Anyanwu ya nemi dakatar da aiwatar da hukuncin tare da daukaka kara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *