Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Kaduna ta tsaida ranar 14 ga watan Janairu, 2025 don fara sauraren ɗaukaka da tsohon Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Aminu, ya shigar kan hukuncin da babbar kotun Jihar Kaduna ta yanke tun a shekarar 2023, in da ta yi watsi da ƙarar da ya shigar ya ya na mai roƙon kotun ta maida shi a matsayin sa tare da biyansa haƙƙoƙinsa da kuma ayyana zaben Sarkin Zazzau na 19 Malam Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin wanda ba’a yi akan tsari ba.
Kotun dai mai Alkalai 3, a ranar Litinin 28 ga watan Oktoba ta zauna inda ta amince da roƙon Lauyan Alhaji Ibrahim Aminu wato Muhammed Tukur Muhammed don karɓar takardun ɗaukaka ƙararsu, daga nan sai kotun ta tambayi lauyoyin wanda ake ƙara wato gwamnatin Jihar Kaduna da mutane 12 cewa ko suna da ja kan roƙon lauyan mai ƙara? Kuma duka suka ce basu da ja. Daga nan ne kotun ta amince da ɗaukaka ƙararsu kuma ta tsaida ranar 14 ga watan Janairu,2025 don fara sauraren shari’ar.
Ina nan daram kan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Zariya – Hamisu Idris
Bita da ƙullin da ake ma Hadi Siriki ya isa haka – Tajuddin Mohammed
Da yake ƙarin haske kan matsayar kotun,lauyan da ke kare wanda ake ƙara Barrister AU Bamalli, ya ce a ka’ida haka ya kamata su yi saboda masu shigar da ƙara sun shigo da shi a ƙurarren lokacin da aka bayar don ɗaukaka ƙara,shiyasa ma aka yi wannan zaman don sauraren roƙon masu ɗaukaka ƙara tun da fari.
Kuma yanzu an basu kwanaki 30 don su shigar da dukkanin takardun su da kuma martani kafin a bayyana a gaban kotun don kare takardun da aka shigar.
Lauyan Turakin Zazzau Alhaji Aminu Shehu Idris wato Barista Buraida Jafaru,ya ce a matsayin su na wanda aka yi ƙara a Kotun,za su cigaba da sanya ido har zuwa lokacin zaman Kotun a gaba don fara sauraren ɗaukaka ƙarar.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.