Wata babban Kotun jihar Kwara, ƙarkashin mai shari’a Justice Hannah Ajayi ta tsare Abdulrahaman Bello da wasu mutane guda 4 da ake zargi da kashe wata ɗaliba mai suna Hafsoh Lawal a ranar 10 ga watan Febrairun wannan shekara da ke aji ƙarshe a Kolejin Ilimi da ke Ilorin a jihar ta Kwara .
Kotun ta sanya ranar 7 ga watan Mayun wannan shekarar domin fara sauraron ƙarar.
Dukkan wadan da ake zargin sun musanta zarge-zarge laifuka biyar da ake musu.
A cikin takardar tuhuma da aka gabatar gaban Kotu, Ana zargin Abdulrahaman ne da wasu mutane 4 da haɗa baki da kuma shirya kashe Hafsoh Lawal tare da sassara gangan jikinta.
Sannan ana zarginsu da haɗa kai wurin cire wasu sassa na jikinta , da kuma kwashe jinin jikinta, baya ga samunsu da wasu sassan jiki mutane da kuma jini.
Mutum na farko da ake zargin, mai suna Abdulrahaman Bello, a bangare guda ana zarginsa da yi gawar ɗalibar fyade , wanda haka ke kasancewa babbar da ke buƙatar ladabtar ga wanda ya aikata ƙarƙashin sashi na 283 na Penal Code CAP P4, na ɓangaren shari’a na jihar Kwara.