April 5, 2025

Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara

Kotun Koli ta rushe hukuncin Kotun Daukaka Kara da ke Abuja, wanda ya amince da Julius Abure a matsayin Shugaban Jam’iyyar Labour Party (LP) na kasa.

A cikin hukuncin da dukkan alkalan kotun suka amince, kwamitin alkalan Kotun Koli guda biyar sun yanke cewa Kotun Daukaka Kara ba ta da hurumin ayyana Abure a matsayin Shugaban Jam’iyyar Labour Party, bayan da ta gano cewa asalin karar na da alaka da shugabancin jam’iyyar.

Kotun Koli ta kuma yanke cewa batun shugabanci al’amari ne na cikin gida na jam’iyya, wanda kotuna ba su da ikon yanke hukunci a kansa.

Har ila yau, kotun ta amince da karar da Sanata Nenadi Usman da wani suka shigar, inda ta bayyana cewa suna da hujjoji.

Bayan haka, kotun ta yi watsi da karar da bangaren Abure na Jam’iyyar Labour Party suka daukaka, bisa hujjar cewa ba ta da tushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *