Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Kswanaki biyu bayan rasa ran wasu mutum 16 a wani hatsarin mota a Abeokuta wasu ukun sun sake rasuwa in da wasu suka jikkata. - Martaba FM Kswanaki biyu bayan rasa ran wasu mutum 16 a wani hatsarin mota a Abeokuta wasu ukun sun sake rasuwa in da wasu suka jikkata. - Martaba FM

Kwanaki biyu bayan mutuwar mutum 16 da suka kone kurmus a wani hadarin mota akan titin Abeokuta zuwa Shagamu, a kalla mutane uku sun rasa rayukan su yayin da wasu 14 suka samu raunuka daban-daban, a wani hadari da ya haɗa da motoci da dama akan babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan.

Jaridar PUNCH ta samu rahoto daga Commandant General na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Ogun Seni Ogunyemi, wanda ya bayyana cewa hadarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba a yankin Ogere na babbar hanyar.

Ogunyemi ya bayyana cewa hadarin wanda ya hada da motoci shidda da fasinjoji 23, ya faru ne lokacin da daya daga cikin motocin ta fadi a gefe yayin da yake juyawa, in da ya zubar da kayan sa a kan titi.

Ya ƙara da cewa sauran motoci biyar, wadanda ba su san abin da ya faru ba, sun fada kan motar da ta fadi saboda gudun wuce sa’a.

Ya ce, “Wani mummunan hadari ya faru a Mile 12 kusa da Ogere akan titin Lagos zuwa Ibadan misalin karfe 8:35 na dare.

“A cewar wani shaida, wata farar babbar mota kirar Benz ta yi hadari ita kadai yayin da take juyawa, inda kayan da take dauke da su suka watse a kan titi. Sauran motoci kuma suka fara kwacewa cikin motar Benz saboda gudun wuce sa’a.”

“Mutane 23 ne suka kasance cikin hadarin. Maza uku sun rasu, sannan mutane 14 maza 11 da mata 3 sun jikkata.”

Ya bayyana motocin da suka hadu da hadarin kamar haka: wata babbar motar DAF mai launin toka ba tare da lamba ba, da wata farar Mazda bus mai lamba LSD72YK, da wata farar babbar mota kirar Benz mai lamba KRD 787 XD.

Sauran motocin sun hada da wata farar Nissan bus mai lamba KTU594YG, da wata koriyar babbar mota kirar DAF da ba ta da lamba, da wata farar Toyota Venza mai lamba ABJ 675 DR.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *