Jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce jam’iyyar PDP mai hamayya a ƙasar ta mutu a fagen siyasar ƙasar.
Yayin da yake jawabi a ofishin jam’iyyar NNPP na jihar Katsina ranar Asabar, jagoran Kwankwasiyyar ya zargi jam’iyyar APC ta jefa kanta cikin abin da ya kira ”halaka”.
”Jam’iyyar PDP dama kowa ya sani a yanzu dai matacciya ce, dama mu ne a cikinta, kuma tun da ta saki layi, muka sake”, in Sanata Kwankwaso.
Ya kuma zargi jagororin gwamnatin APC da nuna halin ko- in-kula game da halin da ƙasar ke ciki, musamman ta fuskar matsalar rashin tsaro.
”Kuna gani yanzu idan kana son fita daga cikin Katsina, duk in da za ka bi, to tunani kake ta inda za ka bi”. in ji shi.
Ƙungiyar Limamai A Najeriya Na Son Gwamnati Ta Gyara Matatun Mai Na Ƙasar.
Zancen Man Fetur Ya Sauka Zai Yi Wahala, -Ɗangote.
Ba ƙwace motocin sojoji ƴan bindiga su ka yi ba – Mazauna Zamfara.
Sanata Kwankwaso ya kuma yi kira ga talakawan Najeriya su kauce wa karɓar taliya ko wasu kuɗi da ya ce ba su taka kara suka karya ba a ranar zaɓe domin sarayar da haƙƙoƙinsu.
”Ku tabbatar cewa ba a sake kawo taliya mutane sun karɓa, sun je sun dafa, sun ci, sun kuma faɗa wahala na shekara huɗu su da ‘ya’ya da jikoki, kun dai ga duka wannan wahalar a kan talaka take ƙarewa,” in ji jagoran Kwankwasiyyar.
BBC Hausa
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Sallamar da Gwamna Abba ya yi wa Sakataren Gwamnati da Kwamishinoninsa 5.
-
Kwankwaso Ya Yi Zargin Ana Neman Yi Musu Dole Daga Lagos A Harkar Masarautun Kano.
-
Rikicin Siyasa Na Kara Yin Zafi A Jam`Iyyar NNPP Yayin Da Kwankwasiyya Ke Rasa Jiga-Jigai.
-
An Sake Kama Wani Mutum Da Bindigogi A Yayin Da Trump Ke Yaƙin Neman Zaɓe.
-
An Ba Wa Ganduje Wa’adin Kwanaki 7 Ya Sauka Daga Shugabancin Jam’iyyar APC.