December 2, 2021

Kungiyar yan jarida ta kasa tayi kira ga hukumomin tsaro dasu taimaka wajan kawar da bata garin yan jarida

Page Visited: 82
0 0
Read Time:1 Minute, 49 Second

Daga Mu’azu Abubakar Albarkawa, Kaduna

 

Kungiyar yan jarida ta najeriya reshen Zaria tayi kira ga masu kula da tsaro dasu taimaka wajen tsaftace harkar jarida da kuma cire masu kiran kansu yan jarida wanda basu dace ba.

Taci gaba da nuna bacin ranta wajan samun hauhawar masu ma aikin jarida karan tsaye a kafafen sada zumunta da kuma yan jaridan da basu cancantaba.

Sanarwan yafitone akarshen taron da kungiyar tayi aranar 14th October 2021, reshen zaria inda takara da nuna bukatar ta na samun cikakken jagoranci kamar yadda take gudanar da aikin ta na kasa.

Kungiyar ta nuna matukar alhininta ta yadda musamman yan siyasa suke goyan bayan masu amfani da kafafen sada zumunta da wasu kafafen watsa labarai wajan watsa magan ganu marasa dadi da kuma labaran karya.

Ta kara da gargadin masu dillancin labarai dasu kiyaye bada tattaunawa ga wakilan kafafen watsa labaran da basu ingantaba, ko kuma daukar hukuncin da aka yankema yin hakan.

Sannan kuma tayi duba akan lamuran tsaro a jihar kaduna da ta dauka matakin dakatar da ayyukan ta addanci da yan fashin daji aciki da wajan jahar wajan hana keke napep da kuma dakatar da mashinan haya a jahar.

Ta kara yin kira da hukumomin tsaro dasu ru6anya ayyukansu wajan sauya matsalolin da yake addabar yan jahar.

Har ila yau sanarwar ta nuna matukar farin cikin ta ga gwabnatin jihar kaduna da hukumomin tsaro wajan nuna rashin gajiyawa ta fuskar dakatar da ayyukan ta addanci.

Ta kuma kara da roko akan hukuncin da gobnati ta yanke na magance tsaro da ta sake duba akai domin sassautama masu mashina na kansu domin gudanar da ayyuakansu na musamman cikin sauki.

Akarshe kungiyar ta taya mai martaba sarkin zazzau, Malam Ahmad Nuhu bamalli murnar cika shekara daya 1, tare da jinjina masa akan gagarimin nasarorin da akasamu acikin shekararsa daya 1 akan karagar mulki.

Sanarwar ta kara da bayyana fatan ta na samun wasu cigaban a shekarunsa na gaba akan karagar mulki.

kungiyar ta rufe jawabin da nada kwamitin mutane uku 3 wanda tasama jagoranci daga Mikail Ibrahim Fagaci na gidan redio nagarta dake kaduna domin samun nasarorin kungiyar a za6en da zata nan gaba na watan November wannan shekarar.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *