October 16, 2024

Kuskuren Jaridar Daily Trust Da Yadda Gaskiya Ta Bayyana Game Da Yarjejeniyar Samoa.

Daga Abdulaziz Abdulaziz

A ranar Laraba da ta gabata jaridar Daily Trust ta fito da jawabin neman afuwa ga gwamnatin tarayya game da labarin da ta wallafa marar tushe kan zargin cewa akwai goyon bayan auren jinsi a cikin yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta Samoa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sanyawa hannu.

Neman afuwar ya biyo bayan rahoton bincike da wani kwamiti mai zaman kansa na sa ido akan aikin jarida ya gabatar wanda ya yi zuzzurfan bincike kan ƙorafin da gwamnati ta shigar game da wancan labari da jaridar Trust ta buga ranar 4 ga watan Yuli na wannan shekarar.

Saɓanin yadda aka saba gani a baya na yadda gwamnati za ta tura jami’an tsaro su kamo ƴan jarida ko su rufe gidan jaridar da ya yi abinda ya ɓatawa gwamnati rai, gwamnatin Tinubu ta bi hanyar laluma domin binciken gaskiyar lamarin da kuma bin haƙƙin ta. Kuma manyan ƴan jarida da ƙwararru ne suka zauna suka yiwa wannan labarin karatun nutsuwa kuma suka nemi bahasi daga Daily Trust, a ƙarshe suka yanke hukuncin cewa jaridar bata da hujjar wancan ikirari don haka ta bawa gwamnatin tarayya haƙuri. Hukumar gidan jaridar ta amsa lefinta, wannan ya sa suka fitar da wancan bayani na bada haƙuri.

A jawabin neman afuwar da ta fitar, Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa ta gamsu da binciken da kwamitin ɗa’ar aikin jarida ya gabatar. Rahoton kwamitin wanda aka fitar a ranar 23 ga watan Satumba, 2024 biyo bayan ƙorafi da gwamnatin tarayya ta shigar. Kwamitin ya gano cewa duk cikin shafuka 403 na yarjejeniyar Samoa babu inda aka yi maganar ƙasashen za su goyi baya ko kare haƙƙin masu neman jinsi a matsayin sharaɗin samun tallafi ko wani taimako daga manyan ƙasashen Duniya. Kuma babu ma inda aka yi maganar masu neman jinsi kwata-kwata a cikin yarjejeniyar.

Tun da farko na kaɗu da jin labarin a matsayina na ƙwararren ɗan jarida. Na yi rubutu a Social Media kan yadda aka samu raunin cika ƙa’idojin aikin jarida musamman ma rashin kafa hujja. Wannan shi ne tsokacin da zan yi ko da ba na cikin gwamnati. Magana ta gaskiya har yanzu ina mamaki ta yaya labarin ya samu wucewa duk da hanyoyin tace labarai da ake da su a ɗakin buga labarai na Jaridar.

Tun farkon fitar labarin kafafen yaɗa labarai da manyan masana aikin jarida da wasu ƙwararru da ma wasu kafafen yaɗa labarai suka fito suka nuna cewa wa ce labarin an gina shi ne bisa tubalin toka, wato dai Daily Trust ta tafka kuskure. A cikin waɗanda suka fitar irin wannan matsaya bayan sun karanta labarin da kuma bin diddigi akwai irin su Farfesa Farooq Kperogi da BBC da jaridun Premium Times da Punch da ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya, da sauransu da dama.

Kasancewarsa abu ne da ya shafi addininmu labarin ya sanya damuwa a zukatan mutane da dama. Babban abinda ya sa kusan kowa ya yadda da labarin shi ne ya zo daga kafar da kowa yana tunanin in dai labari ya fito daga gare ta gaskiya ne.

Labarin ya fita ranar Alhamis, kuma tada ƙurar da ya yi ya sanya hakan ya sanya mutane da dama a Arewa musamman Malamai suka yi huɗubobi masu zafi a ranar Juma’a. Banga laifinsu ba saboda labarin ya zo ne daga kafar Daily Trust da aka aminta da ita.

Bayan mutane sun fusata, wasu kuma daga ƴan adawa sun ƙara rura wutar. Wasu ƙusoshin ƴan adawa sun yi ta kiran wasu malamai suna roƙonsu kan lallai su fito su ƙalubalanci gwamnati. Wannan ne babban babban abinda ya janyo limamanmu masu daraja suka hau mimbari a fusace da labarin da ba shi da tushe. Shugaba Tinubu da gwamnatinsa da dukkaninmu haka aka yi mana tofin ala-tsine ba tare da bin diddigin zancen ba. An zargi gwamnati da siyar da Najeriya domin ɗaga darajar masu neman jinsi, da dai sauran kalamai marasa daɗi da aka yi a cikin fushi.

Mun sha takaici ƙwarai ganin yadda duk ƙoƙarin nuna gaskiyar abin mutane da dama suka toshe kunnuwansu. Na sha tambayar mutane ko sun san cewa ba inda wannan yarjejeniyar ta sauya dokokin mu da suka haramta auren jinsi? Kuma ta yaya sanya hannu a dokar ya bawa masu auren jinsi wani ƴanci? Ba wanda zai baka amsar wannan tambayoyi, sai dai kame-kame, saboda kawai yarda da wancan rahoton na ƙarya.

Wannan abin da ya faru babbar fadakarwa ce ga nauyin da yake kan ƴan jarida na tabbatar da hujja da tantance gaskiya. Illar da rashin yin hakan zai iya jawowa ba ƙarama ba ce domin kuwa kamar masu iya magana ke cewa, ita magana zarar bunu ce; matuƙar ta fita mayar da ita abu ne mawuyaci.

Aikin jarida aiki ne da ke buƙatar lura da taka-tsantsan da tafiya bisa hujja. A lokacin da yake ƙaddamar da kamfanin Sardauna da yake ƙaddamar da tawagar jaridar Najeriya yayi musu gargaɗi da cewa “ku faɗi gaskiya a kan mu, kuma ku faɗa mana gaskiya akan wasu”. Ba abin da muke buƙata fiye haka.

Abdulaziz, babban mataimaki na musamman ne ga shugaban ƙasa kan yaɗa labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *