January 22, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Kutu ta ɗaure likitan bogi da ya yi shekaru 10 ya na aiki a Abuja.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

Wata babbar kotu da ke Jabi a babban birnin tarayyar Nigeria Abuja, ta samu wani mutum mai Martins Ugwu da laifin yin ƙarya da amfani da takardun shaida na abokinsa, George Daniel Davidson, don samun aiki a ma’aikatar lafiya ta tarayya.

A cikin wata sanarwa a ranar Talata, mai magana da yawun Hukumar Yaki da Rashawa da sauran laifuka masu alaka da ita (ICPC), Demola Bakare, ya ce hukumar ta gabatar da ƙarar da ta ƙunshi tuhume-tuhume bakwai kan Ugwu a watan Fabrairun shekarar 2016.

Bakare ya bayyana cewa an gurfanar da Ugwu a kotu bisa zargin bayar da bayanan karya ga shugaban hukumar ma’aikata ta tarayya, wanda ya ba shi damar samun aikin gwamnati a shekarar 2006.

Wanda ake zargin ya kwashe tsawon shekaru 10, ya samu albashi da alawus na Naira miliyan 17.2 tare da gabatar da kansa a matsayin likitan da ya kware a fannin lafiya, alhali ba haka ba ne.

Wannan laifi ya saba wa sashi na 25(1)(a) na dokar yaki da rashawa da sauran laifuka masu kama da ita ta shekarar 2000.

Bakare ya kuma bayyana cewa Ugwu ya yi amfani da takardun bogi wajen samun katin shaida na ma’aikaci, neman hutun shekara-shekara, da yin rajista a wani shirin digiri na biyu (postgraduate) a fannin nazarin cututtuka (epidemiology), wanda zai iya ba shi damar samun digirin digirgir (master’s degree).

A lokacin zaman yanke hukunci, lauya mai gabatar da ƙara na ICPC, Osuobeni Ekoi Akponimisingha, ya roƙi kotu da ta umarci Ugwu ya dawo da naira miliyan 17.2 da ya samu ta hanyar yaudara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *