Daga Sani Ibrahim Maitaya
Shugaban rundunar tsaro ta kasa Christopher Musa, ya sanar da cewa kwanaki kaɗan ne suka ragewa riƙaƙƙen ɗan ta’adda Bello Turji a duniya.
A cewar Christopher Musa aikin yaƙi da ta’addanci da rundunar soji ke yi a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan, ya jefa fargaba da tsoro ga sansanin Bello Turji da gungun shi.
Ya kara da cewa take-taken riƙaƙƙen ɗan ta’addan sun nuna irin yadda ya firgita.
Janar Christopher Musa ya bayyana hakan ne, a wata ganawa da aka yi dashi a Abuja a wurin taron lakca ta kasa-da-kasa da ake gudanarwa a duk shekara.
Ya ƙara da cewa a yanzu dai Turji ya ce an halaka kwamandan shi, kuma ya tabbatar da cewa shine kan layi, babu abun da yake face sanbatu.
Kalamai na Janar Christopher Musa, na zuwa ne bayan fitar wani faifan bidiyo da shi Bello Turji ya yi a ranar talatin ga watan Satumba, mai tsawon mintuna biyar da sakan arba’in.
Najeriya Ta Fi Samun Tsaro A Mulkin Tinubu -Nuhu Ribadu.
Sojojin Nijar Sun Kashe Ƴan Bindiga 60
Biyan kudin fansa ba ya hana ƴan bindiga kashe wanda aka yi garkuwa da shi – Gwamna Radda.
An dai ga shi Bello Turjin ya na magana cewa masu buƙatar a kashe shi su sani cewa dama ba su zo duniya ba domin su share wuri su zauna ba, kuma ba gare su farau ba, ya na mai cewa tun lokacin annabawa da sahabbai ake kashe su, ya na mai cewa basa tsaron a kashe su.
A cikin bidiyon an kuma ji yadda ya yi gaisuwar ta’aziyya akan mutuwar uban gidan shi watau Halilu Buzu Sububu, tare da cewa kashe shi ba shine da muhimmanci ba, sannan ba shine zai firgita su ba, kana ya ba da tabbacin cewa kalma ɗaya ce ba’a fahimta ba, shine a daina kashe musu ƴan uwa Fulani musamman a yankin jahohin Sakkwato, da Kebbi, da Zamfara sannan su daina kashe Hausawa.
Kawo yanzu dai ana ci gaba da ɗaukar mutane domin karbar kudin fansa a wasu sassan jahar Zamfara, duk irin nasarar da dakarun soji ke iƙirarin su na samu akan yan ta’addan.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƴansanda Sun Kama Wani Ɗan Kasar Aljeriya Da Bindigu A Zamfara.
-
Akwai Bindigogin AK47 Guda Dubu 60 A Sansanonin Ƴan Bindiga Ɗari 120 Cikin Jihohin Arewa Masu Yamma,-Rahoto.
-
Wani Babban Kwamandan Sojin Isra’ila Ya Baƙunci Lahira A Gaza.
-
An Sake Kama Wani Mutum Da Bindigogi A Yayin Da Trump Ke Yaƙin Neman Zaɓe.
-
Mutum Sama Da 20 Sun Mutu A Wani Harin Da Sojoji Su Ka Kai Kasuwa A Sudan.