Hukumar Kwastam ta Najeriya a ranar Litinin ta sanar da cafke lita dubu ashirin da takwas da dari uku na man fetur, a Rundunar Yankin A na Hukumar.
Da yake magana yayin da yake nuna man fetur da aka kama ga ‘yan jarida a Makarantar Horas da Kwastam da ke Ikeja, Kwanturola Janar na Hukumar Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa Jihar Ogun ce ke da kaso mafi tsoka na fasa kwauri na man a Yankin Kudu maso Yamma da kashi 65, yayin da Jihar Legas ke da kashi 35.
A cewar sa, cikakken bincike kan yadda ake yin wannan fasa kwauri a yankin ya bayyana dabarun da masu fasa kwauri ke amfani da su da kuma hanyoyin da suka fi bi.
Ya kara da cewa yankin Imeko-Afon a Jihar Ogun yana da kashi 25% na jimillar kame-kamen, yayin da Ilaro-Ojodan ke da kashi 22%, sai kuma hanyar Owode-Ajilete da ke da kashi 18%, wanda ke kawo jimillar kashi 65%.
“Korido na farko shi ne yankin Badagry-Seme, wanda ke da kusan kashi 35% na dukkan kamun da aka yi,” in ji Adeniyi.
Shugaban Kwastam ya jaddada cewa wannan yanki ne mafi hatsari dangane da safarar man fetur, inda aka samu kama mai yawa a kan hanyar Badagry-Seme da kuma bakin ruwan ta.
Ya ce kusancin wannan yanki da Jamhuriyar Benin da kuma yawan hanyoyin ruwa a wurin, na sa ya zama hanya mafi sauki ga masu fasa kwauri.
“Korido na biyu da aka gano shi ne yankin Imeko-Afon a Jihar Ogun da ke da kashi 25% na kamun, yayin da Ilaro-Ojodan ke da kashi 22% da kuma Owode-Ajilete da ke da kashi 18%,” in ji shi.
Adeniyi ya jaddada cewa waɗannan hanyoyi na ƙara zama sabbin wuraren da masu fasa kwauri ke amfani da su don kaucewa wuraren da jami’an tsaro ke sintiri.
Game da kayayyakin da aka kama, Adeniyi ya bayyana cewa aikin da aka gudanar daga ranar 11 ga watan Janairu zuwa 23 ga watan Fabrairu 2025 ya kai ga cafke lita 28,300 na man fetur da ake ƙoƙarin fitarwa ta hanyoyi daban-daban.
Ya bayyana cewa kuɗin harajin da za a biya kan wannan mai da aka kama ya kai Naira miliyan 35 da dubu dari takwas.
Har ila yau, ya ƙara da cewa an kama motoci uku da masu fasa kwaurin suka yi amfani da su wajen safarar man.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An banka wa gidaje 24 da runbunan ajiyar hatsi wuta a jihar Jigawa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani.
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.