Lauyan kare haƙƙin bil’adama Femi Falana, ya yi gargaɗi kan kowane irin bincike da hukumomin tsaro za su gudanar kan yadda Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar, ta samu damar halartar taron Kungiyar Majalisun Duniya (IPU) a birnin New York.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Babban Lauyan Najeriya ya ce binciken da hukumomin tsaro za su yi kan lamarin, zai iya jawo wa Najeriya abin kunya da raini maras amfani.
Jaridar PUNCH ta yanar gizo ta ruwaito cewa, Akpoti-Uduaghan ta yi jawabi a taron IPU a ranar 11 ga watan Maris, inda ta yi magana kan dakatar da ita daga majalisar dattawa bisa zargin rashin da’a.
Sanatar ta bayyana cewa an dakatar da ita ne domin a hana ta magana, kan zarge-zargen cin zarafin mata da tayi wa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio.
A yayin wani zama na majalisar dattawa a ranar Talata, Akpabio ya mayar da martani yana mai cewa, halayen sanatar a taron IPU ya kunyata gwamnatin Najeriya da al’ummar ƙasar gaba ɗaya.
Rahotanni sun bayyana a ranar Lahadi cewa, Hukumar Tsaro ta farin kaya ta kasa (DSS) da Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), sun kaddamar da bincike kan yadda Sanatar Kogi ta samu damar halartar taron ba tare da an tura ta a hukumance ba.
Sai dai Falana yayi gargaɗi cewa, wannan bincike zai iya jawo wa wasu manyan jami’an gwamnatin Bola Tinubu abin kunya.
Bayanin ya ci gaba da cewa “A ƙarshe, abu ne da kowa ya sani cewa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya zargi Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da kunyata gwamnati da al’ummar Najeriya, ta hanyar kai karar dakatar da ita zuwa ga Kungiyar Majalisun Duniya (IPU).
“Akasin abin da Shugaban Majalisar Dattawa ke tunani, shi ne binciken da hukumomin tsaro za su yi game da tafiyar sanatar zai jefa Najeriya cikin abin kunya da raini maras amfani” Inji shi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙudirin dokar da ke neman samar da Ofishin Firainista a matsayin Shugaban Gwamnati a Najeriya ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilai.
-
Jami’an tsaro sun kama ɗalibai 59 a jihar Oyo
-
An dawo da ƴan Najeriya kusan 1000 gida daga ƙasar Libiya a farkon 2025 kawai
-
Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe kan soke hawan Sallah.
-
Kwastam ta kwace kuɗi kimanin naira biliyan 289 da aka boyi a katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Saman Abuja