Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Majalisar Dattijan Najeriya ta buƙaci rundunar sojojin ƙasar da sauran hukumomin tsaro su ƙaddamar matakan katse hanzarin ƙungiyar ƴan bindigar nan ta Lakurawa.
BBC Hausa ta rawaito, majalisar ta kuma yi kira da a ɗauki dukkan matakan da suka dace domin hana su faɗaɗa ayyukansu a yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Ƴansanda Sun Kama Wani Ɗan Kasar Aljeriya Da Bindigu A Zamfara.
Ƴan bindiga Sun Sanya Harajin Miliyan 10 Ga Wasu Ƙauyuka A Jihar Katsina.
Ta kuma nemi a ci gaba da sa-ido a yankunan da Lakurawan suka mamaye, inda ta yi gargaɗin cewa a ɗauki matakan da suka dace, domin a cewarsu, haka Boko Haram ta fara.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An banka wa gidaje 24 da runbunan ajiyar hatsi wuta a jihar Jigawa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani.
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.