Daga Umar Rabi’u Inuwa
Majalissar dokokin jihar kano da ke Arewacin Najeriya, ta nuna rashin amincewa da sabon ƙudirin dokar haraji da gwamnatin tarayya ta aikewa majalissun ƙasar.
Shugaban masu rinjaye na majalissar kuma ɗan majalissa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa shine ya gabatar da kudirin a yayin zaman majalissar na yau.
Lawan ya ce, amincewa da dokar zai haifar da matsanancin talauci da ƙaruwar ƙalubalen tsaro ga arewacin ƙasar nan.
Gwamnan Kano ya gana da ƴan majalisar wakilai na Kano Kano sabuwar dokar haraji.
Da ya ke goyon bayan kudirin ɗan majalissa mai wakiltar Ungogo Alhaji Aminu Sa’ad Ungogo ya ce Idan majalissun ƙasar suka amince da dokar kuɗaɗen harajin za su tafi ne zuwa jihohin Lagos da wasu jihohin kudu ya na mai cewa an shirya hakan ne domin haifar da matsaloli a yankin Arewa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta ficewar Nijar daga rundunar hadin gwiwa ta MNJTF.
-
CBN ya ƙaryata fitar da takardun kuɗi ƴan dubu 5 da dubu 10
-
Gwamnatin jihar Kebbi ta musanta yi wa ƴan luwaɗi da maɗigo rajista a jihar.
-
Ɗan banga ya harbe kansa a ƙoƙarin bin wanda ake zargi da aikata laifi a Abuja.
-
Sarkin Musulmi ya shawarci gwamnonin Najeriya da su kawar da bambanci tsakanin ƴan asalin jiha da baƙi.