April 1, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Majalisar dokokin jihar Rivers ta musanta karɓar wasiƙar miƙa kasafi daga gwamna Fubara.

Majalisar Dokokin jihar Rivers ta musanta cewa ta karɓi wata wasika daga Gwamna Siminalayi Fubara, dangane da gabatar da kudurin kasafin kuɗin 2025 a gaban majalisar.

Gwamna Fubara a cikin wata wasika mai kwanan wata Alhamis 13 ga watan Maris 2025, da ya aike wa Kakakin Majalisar Rt. Hon. Martins Amaewhule, ya nuna sha’awar sa ta gabatar da kasafin kuɗi a ranar Laraba 19 ga watan Maris 2025 ko kuma wata rana cikin watan na Maris.

Sai dai mambobin majalisar da ke goyon bayan Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja Cif Nyesom Wike, sun dakatar da zaman majalisa ba tare da ƙayyade ranar dawowa ba, yayin zaman da suka yi a ranar Juma’a.

Amma yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Lahadi a Fatakwal, Shugaban Kwamitin Yada Labarai na majalisar Hon. Enemi Alabo George, ya zargi Gwamna Fubara da ƙin aiwatar da hukuncin Kotun Koli kan rikicin siyasa da ke jihar, musamman umarnin da ke buƙatar ya sake gabatar da kasafin kuɗi ga yawancin ‘yan majalisa.

George ya buƙaci jama’a su matsa wa gwamnan lamba don ya bi doka wajen gabatar da kasafin kuɗin, maimakon ƙoƙarin samun tausayi ta hanyar nuna ‘yan majalisa a matsayin masu kawo cikas.

Ya ƙalubalanci Fubara da ya gabatar da kwafin wasikar da ya ce ya aika wa majalisar, mai ɗauke da sa hannun karɓa daga majalisar.

Ya ce: “A makon da ya gabata, an ce yayin da gwamnan ke kan hanyar sa zuwa Ogoni domin wani buki, ya tsaya a ƙofar Majalisar Dokokin don yi wa manema labarai jawabi.

“A cikin jawabin nasa, ya yi ikirarin cewa ya aika da wata wasika ga majalisar yana bayyana aniyyar sa ta zuwa don gabatar da kasafin kuɗi. Wannan batu ya ba mu mamaki sosai, domin babu irin wannan wasika da aka karɓa a majalisar”.

“A bayan nan, wasu daga cikin hadiman sa sun ce sun aika da wasikar ta hanyar WhatsApp ga wasu mambobin majalisa, abin da muka ɗauka a matsayin abin kunya da rashin ƙwarewa.

“Yanzu haka, shafukan sada zumunta sun cika da labaran wata wasika daga gwamna zuwa majalisa, amma wannan ba gaskiya ba ne”.

“Muna kalubalantar gwamna da hadiman sa da su fito da kwafin wasikar da aka karɓa ko kuma wata hujja da ke nuna cewa an aike da ita, kuma an karɓa. Wannan magana ba gaskiya ba ce, kuma jama’a su yi watsi da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *