Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da Dokar Kafa Hukumar Wutar Lantarki ta Kano (Kano State Electricity Agency Bill 2025) domin inganta samar da wutar lantarki ga al’ummar Kano, Katsina da Jigawa ta hanyar amfani da madadin hanyoyin makamashi irin su hasken rana (solar), iska da ruwa.
An karanta kudirin dokar karo na uku a zaman majalisar ranar Litinin, karkashin jagorancin Kakakin Majalisa, Rt. Hon. Ismail Falgore, in da aka tantance ta a kwamitin gaba ɗaya kafin amincewa da ita.
Shugaban masu rinjaye, Hon. Lawan Hussaini, ya bayyana cewa dokar za ta taimaka matuka wajen rage wahalhalu da tsadar makamashi, da kuma habaka karamin da babbar masana’antu. Haka kuma za ta taimaka wa asibitoci da cibiyoyin tace ruwa su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ya ce za a kafa hukumar ne da shugabanta, babban darakta da mataimakinsa, inda kowace jiha za ta samu wakilai uku. Shugaban hukumar za a rika sauyawa tsakanin jihohin kowanne bayan shekara huɗu.
“Babban darakta dole ne ya kasance da gogewar shekaru goma a fannin samar da lantarki da rarraba makamashi,” inji Hussaini.
Majalisar ta buƙaci taimako ga waɗanda ambaliya ta shafa a Doguwa.
A wani bangare na zaman, majalisar ta bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya hanzarta kai kayan agaji ga sama da gidaje 200 da guguwar ruwan sama ta lalata a yankin Doguwa.
Wakilin Doguwa a majalisa, Hon. Salisu Mohammed, ya bayyana cewa al’ummomin Bahuwa, Rafin Dadi, Maraku da Asada da ke cikin Ungwar Tshohuwa ne abin ya shafa. Ya ce gine-gine da makarantu da masallatai sun samu mummunar illa, duk da cewa ba a rasa rai ba.
Majalisar ta buƙaci gwamnatin jihar da ta gaggauta daukar mataki don tallafawa jama’ar da ambaliya ta shafa.