Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Ƙungiyar Malaman Kwalejin Fasaha reshen Jihar Kano, ta shiga yajin aikin gargaɗi na mako biyu da zai fara daga ranar 2 ga Disamba, 2024.
Wannan mataki an bayyana shi ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar, Babangida Sa’adu, da ya sanya hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano.
An yanke shawarar shiga wannan yajin aikin ne a taron NEC na 112 na ASUP da aka gudanar a Abuja ranar 28 ga Nuwamba, 2024
Gwamnatin Kano ta dawowa da Jami’ar Yusuf Maitama University sunanta na asali Northwest University.
Kungiyar ASUU reshen jihar Bauchi ta shiga yajin aikin sai baba ta gani.
ASUU ta nuna damuwa kan yawaitar ɗaliban da ke samun sakamakon first-class a Najeriya.
A lokacin wannan yajin aiki, dukkanin harkokin karatu a Polytechnic ta jihar Kano za su tsaya cik.
ASUP ta ta ba bai wa gwamnatin tarayya da sauran hukumomin da abin ya shafa wa’adin kwana 15 don sake duba da janye manufofin da su ka saɓa wa dokar Polytechnics da sauran dokokin gudanarwa a wannan bangaren.
Kungiyar ta zargi Gwamnati da rashin ɗa’a da kuma raina wasu muhimman dokokin da su ka kafa manyan makarantu mallakin jihohi da sauran kayan aikin gudanarwa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƴansanda sun kama mutane 7 da ake zargin ƴan kungiyar asiri ne a Ogun.
-
Benue: Mutane 20 sun mutu, an ceto mutane 11 a hatsarin kwale-kwale.
-
Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.
-
Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane tare da ƙwato alburusai a Filato.
-
Mun mayar da yara miliyan 1.5 makaranta a Borno – Zulum.