August 8, 2022

Manufata ga Jihar Jigawa (I)

Page Visited: 171
0 0
Read Time:5 Minute, 58 Second

Daga Mustapha Sule Lamido

 

A rayuwar kowacce al’umma, a kan samu lokuta daban-daban da matsaloli suke mata katutu ta yadda har sai an buƙaci gudunmawar mutane masu manufa domin warwaresu. Waɗannan matsaloli su kan yi tsanani har wasu su ga kamar ba za a iya shawo kansu ba har ma a dinga tunanin ko zasu yi sanadiyyar rushewar wannan al’umma baki ɗaya. Kasashe su kan samu kansu a wannan yanayi cikin tarihinsu. A yanzu Najeriya tana cikin wani mawuyacin hali da aka jima ba a ga irinsa ba, Jigawa da sauran jihohi su ma basu tsira daga wannan yanayi ba. Wannan ita ta sa ya zama dole ga dukkan wasu mutane da suke da wasu dabaru kan yadda za a magance wasu daga cikin waɗannan matsaloli, su sadaukar da kansu ga aikin al’umma duk kuwa da irin takurar da zasu samu kansu a ciki.

Koda yake an haife ni a gidan siyasa kuma na taso a cikinta tsawon rayuwa ta, amma ban yi tunanin tsayawa takara ba kai tsaye sai a ƴan shekarunnan. Duk da irin ƙalubale da gutsuri-tsoman da hakan ya jawo min, ko kaɗan ban yi nadamar shiga siyasar takara ba. Daga takarar Sanata a 2019 zuwa wannan da nake yi ta gwamna yanzu, na bibiyi ra’ayoyin jama’a daban-daban. Da masu suka na da masu yabo na, duk na girmama ra’ayinsu tare da yanke shawarar cewa sun ƙare ni da wani ilimi wanda a da ban san shi ba. In da wani abu mai wahala da na koya a siyasa, shi ne babu abin da zaka iya canzawa idan kana gefe har sai ka fito an dama da kai kai tsaye. Wani abu kuma da na fuskanta shi ne matasa iri na suna shan wahala sosai wajen gamsar da mutane cewa zasu iya gudanar da mulki idan an basu dama.

Kusan kowa yana da labarin cewa ni ne ɗan takarar gwamnan Jihar Jigawa a tutar Jam’iyyar PDP kuma tuni hukumar zaɓe ta INEC ta tabbatar da hakan. Saɓanin yadda wasu suke tunanin ko na samu hakan a ɓagas, to ba haka bane. Wannan nasara da Allah Ya bani, ta zo ne bayan aiki tuƙuru, jajircewa, bibiyar al’amuran jama’a da na ƴan jam’iyya na ƙasa da ni da ƴan tafiya ta muka dinga yi na tsawon shekaru sama da biyu. Irin wannan jajircewa da na yi amfani da ita wajen samun takara, ita nake so na nunnunka domin cin nasara a babban zaɓe da kuma yi wa jama’ar Jigawa aiki tuƙuru idan Allah ya bamu nasara.

Na fahimci cewa akwai masu ganin kamar ina neman mulki ne domin na ɗauke shi kamar gado, masu wannan tunani suna ganin haka ne saboda basu samu damar karanta manufofina ba. Nan ba da jimawa ba zan yi taron ƙaddamar da daftarin manufofina ga jama’a, sai dai ba lallai ne wannan daftari ya kai ga kowa ba, don haka ne na yanke shawarar wallafa irin waɗannan ƙasidu cikin harshe mai sauƙi domin jama’ar da nake so su ɗauke ni aiki su fahimci inda na sa gaba. Kuma zan yi bakin ƙoƙari domin ganin wannan saƙo nawa ya isa lunguna da saƙo. Ina da yaƙinin cewa da zarar na gama wallafa manufofina, mafi rinjayen ƴan Jigawa zasu gamsu cewa ba wai kawai ina da burin zama gwamna don kawai a ce min gwamna ba ne ko kuma a‘a ina da burin in gaji mahaifina ba ne kawai. Allah Ya sani, ƙuduri na shi ne ci gaban Jigawa, to amma ba yadda zaka iya ga waɗanda suke da mummunar fahimata a kan ka. Abin da kawai na haƙiƙance shi ne, sannu a hankali, zan ba wa maraɗa kunya da yardar Allah.

Babban burina a matsayin gwamna shi ne na assasa fandisho mai ƙarfi wanda zai haɗa kan ƴan Jigawa kuma ya ɗora jihar a kan turbar ci gaba mai ɗorewa, Jigawa wacce ta ke da arziki na ƙashin kan ta ba tare da ta dogara da Gwamnatin Tarayya ba, Jigawar da watarana za ta yi gogaggya da jihohin Lagos, Kano da Ogun. Ina da ƙudurin neman dukkan goyon bayan da zai taimaka wajen maida mutanen Jigawa uwa ɗaya uba ɗaya masu ƙauna, kishi da girmama juna. Ta hanyar manufofi masu kyau da zamu shimfida, ina mafarkin Jigawa zata zama ta kowa ba tare da wariya ko rarrabuwar kawuna ba, jiha mai haɗin kai a kan manufar kawo ci gaba.

Idan mutanen Jigawa suka ba ni dama, zan yi aiki da dattawa da dukkan masu ruwa da tsaki na Jihar daga dukkan jam’iyyu domin haɗa kan mutanen mu daga dukkan masarautu. Da izinin Allah, gwamnatina za ta samar da dama da yanayi mai kyau inda mutumin Dutse ko Ringim zai dinga ganin mutumin Hadejia, Kazaure ko Gumel a matsayin ɗan uwansa wanda yake so da ƙauna kamar sun fito daga masarauta ɗaya. Wannan rarrabuwar kai da muke fama da shi yanzu ba shi da wani amfani kuma an ƙirƙire shi ne domin raba kan mutane tare da kautar da hankulansu daga ainihin matsalolinmu.

Tsawon shekaru huɗu da suka gabata, ina ta aiki da masu ruwa da tsaki a cikin da wajen PDP domin samar da daftarin tsarin ci gaban Jihar Jigawa na shekaru 35 kamar yadda aka yi wa Jihar Legas. Ina farin cikin shaida muku cewar yanzu haka wannan daftari ya kammala. Burina shi ne, idan kuka zaɓe ni, zan kira gangamin taron masu ruwa da tsakin jiharmu domin bada dama ga dukkan ƴan jiha su tsefe daftarin domin bada gudunmawarsu. Sarakunanmu, ƴan siyasa, ƙwararru, malamai da ƴan kasuwa duk zasu bada shawarwari akan daftarin wanda idan ya kammala za a tura shi Majalisar Dokoki domin ya zama doka. Da ya zama doka, to kowanne gwamna da zai zo ba shi da zaɓi sai dai ya aiwatar da shi domin manuofofi ne na mutanen Jigawa.

Idan kuka bani dama, gwamnatina zata tabbatar da adalci wajen rarraba aiyuka da alkhairan gwamnati. Ba zan fifita kowanne gari a kan wani ba, haka kuma ba zan bari a fifita wasu mutane ko a tozarta wasu ba. Ni ɗan Adam ne, tare nake ban cika goma ba, amma zan yi duk mai yiwuwa wajen ganin ban bari an nuna wa wani ɗan Jigawa wariya a cikin Jiharsa ba. Zan ƙirƙiro tare da aiwatar da manufofin gyara ga ma’aikatun gwamnati domin su kasance masu yi wa jama’a aiki.

Daga nan zuwa zaɓe, zan dinga tattauna manufofina da jama’ar Jigawa tare da burin cewa hakan zai gamsar dasu kan kyawawan ƙuduori da tsare-tsaren da suka sa nake so su bani dama na yi musu aiki a matsayin gwamna. Ina rokonsu dasu saurareni kuma su fahimce ni domin su samu gamsasshiyar hujjar da zusu yi min alƙalanci a kakar zaɓen 2023 mai zuwa.

A ƙasida ta ta gaba, zan ɗora a kan wannan gabatarwa, zan bada cikakkun bayanai kan yadda zamu gina haɗaɗɗiya kuma ingantacciyar Jigawa. Rubuce-rubucena na gaba zasu fayyace manufofina a sauƙaƙe tare da kawo bayanai akan tsare-tsarena game da ilimi, tattalin arziki, kiwon lafya, tsaro, muhalli da kuma ci gaban addini da zamantakewa.

Gobe Ta Allah Ce

©Santurakin Dutse.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *