Daga Suleman Ibrahim Moddibo
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wata mata mai suna Maryam Usman ƴar shekara 26 wadda ta kashe kanta a unguwar Sheka da ke ke jihar.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai inda ya ce, lamarin ya faru ne a “ranar 13 ga watan ɗaya na wannan shekara ta 2022 da misalin karfe 6 na yamma mun samu rahoto marar daɗi daga unguwar Sheka, a kan cewa wata mata mai suna Maryam Usman ƴan kimanin 25 da ke wannan unguwa ta ciji mahaifin ta a hannu wanda kuma bayan sun kulle ta a ɗaki sannan ta sa baki ta cire yatsanta ta fasa gilas din ɗakin wato window ta cakawa kanta a wuya ta faɗi aɗakin.”
Kiyawa ya ƙara da cewar “kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano Sama’ila Sha’aibu Dikko, ya ta da dakarun ƴan sanda da gaggawa zuwa wannan gida wanda aka ɗauke ta da wuri aka garzaya da ita babban asibitin Murtala wato da ke nan cikin garin Kano wanda likita ya tabbatar da cewa ta rasu.”
Daga tambayoyi da muka yiwa iyayenta sun tabbatar da cewa ta dawo ne daga gidan mijinta saboda laluri na rashin lafiya wanda a wannan ranar ma ta dawo daga asibiti, bayan ta dawo daga asibiti ta faɗa a gidan a kan cewa a maida ita gidan mijinta ta karbo takarda,” inji Kiyawa.
A cewar sa bayan tayi wannan maganar ne tayi tsallake ta ciji mahaifinta da suka ga abinda ta yi shine suka yi yunkuri suka kulleta a ɗaki kuma ta je ta aikata wannan aika-aika.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An Yi Ƙarar Buhari Kan Batan Kuɗin Wutar Lantarki Naira Tiriliyan 11.An Yi Ƙarar Buhari Kan Batan Kuɗin Wutar Lantarki Naira Tiriliyan 11.
-
Zamu Rufe Tashoshin Jirgin Sama Dana Ƙasa Da Titunan Idan Ba’a Janye Yajin Aikin ASUU – Ɗalibai.
-
Gwamnati Ta Ayyana Masu Amfani Da Makami Suna Kwacen Waya Amatsayin Yan Fashi- YAPS.
-
Yadda muka tsira daga sansanin ƴan ta’adda tareda ƴaƴan mu – Ƴan matan Chibok da suka kuɓuta.
-
Gaskiyar Bidiyon Ɗan Najeriyar Da Ya Yi Kuka A Raudar Annabi, Wanda Hakan Ya Jawo Ce-Ce-Ku-Ce.