August 8, 2022

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Matashin Da Ake Zargin Ya Yi Wa Ƙanwarsa Fyade Sau 2 A Gombe.

Page Visited: 5844
3 2
Read Time:1 Minute, 8 Second

Ƴan sanda a jahar Gombe sun kama wani matashi mai suna Abubakar Hamidu, ɗan shekaru 35 da ke zaune a Unguwar Jauro Abare, da zargin yiwa ƙanwarsa fyade har sau biyu a lokuta daban-daban.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe, Ishola Babatunde Baba’ita, ya ce wani mai suna Muhammad Hamza ne ya shigar da karar matashin a ranar 19 ga watan Yulin da muke ciki.

Baba’ita ya ce mai shigar da karar wanda ke zaune a Unguwar Kasuwar Mata, ya kai wa ’yan sanda korafin cewa wanda ake zargin ya yi lalata da kanwar tasa ce karon farko a wani gida da ya zama kufai a Unguwar ta Jauro Abare.

Tsaro: Aikata Miyagun Laifuka Ya Ragu A Jihar Gombe A Watan Janairu.

Zamu Kawo Ƙarshen Ta’addanci, Bangar Siyasa, Fyade, Cin Zarafin Jinsi – Sani Albani

Kungiyar Mafita ga Matasan Arewa Maso Gabas ta kaddamar da littafi kan Illar Fyade da Fataucin Mutane

Kwamishinan ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan, ASP Mahid Mu’azu, ya ce an sake kama matashin karo na biyu yana aikata masha’ar da kanwar tasa a bakin wani tafki.

A cewarsa, da zarar sun kammala bincike za su tura wanda ake zargin zuwa kotu domin ya fuskanci shari’a.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *