December 2, 2021

Maulidi: Gwamna Inuwa Yahaya ya bukaci Musulmai su dauki darussan cikin sa, da koyi da halayen Annabi Muhammad (SAW)

Page Visited: 97
0 0
Read Time:1 Minute, 33 Second

 

A yayin da Musulmai a Jihar Gombe suka bi sahun sauran Musulmai a faɗin duniya don murnar bikin Mauludi na bana a yau Talata 19 ga watan Oktoban 2021, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya aike da sakon taya murna ga al’ummar Musulmi, inda ya buƙaci su yi amfani da wannar damar don ɗaukar darasi, da jajircewa kan kyawawan dabi’u na hidima, da zama tare cikin lumana da jagoranci abin koyi na Annabi Muhammadu (SAW).

A cikin wata sanarwa don murnar zagayowar wannar rana ta haihuwar Manzon Allah S.A.W, Gwamna Inuwa ya kuma yi nasiha ga al’ummar Musulmi kan cusa ruhin juriya da tawali’u da ladabi da karamci a zukatan su, kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar a lokutan rayuwar sa.

Yace “Yayin da muke tunawa da wannar babbar rana, ina kira a gare mu, da mu ci gaba da dabbaka wadannan halaye da dabi’u a rayuwar mu, wadanda manzon Allah mai daraja yayi wasiyya dasu ga ɗan adam a cikin ɗabi’u da mu’amalolin mu don amfanin al’ummah”.

Gwamnan ya kuma buƙaci a ci gaba da addu’o’in neman zaman lafiya da ci gaban Jihar Gombe da kasa baki daya.

“Ya kamata bikin Maulidi ya sabunta mana imanin mu tare da haɗa kai don yin addu’ar zaman lafiya da ci gaba da kwanciyar hankali ga jihar mu da ƙasa baki daya don cimma burin mu na ci gaba.”

Ya kuma bukaci shugabanni da jagorori su yi duk mai yiyuwa don tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da ci gaban al’ummah.

Gwamna Inuwa wanda ya jaddada buƙatar haƙuri a tsakanin al’ummu daban-daban na jihar, ba tare da la’akari da banbancin dake tsakanin su ba, ya buƙaci su ci gaba da kasancewa masu bin doka da kuma kishin zaman lafiya da kwanciyar hankali da Jihar Gombe ke dashi ta hanyar gujewa duk wasu ayyukan daka iya kawo ɓaraka.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *