August 8, 2022

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Mawakan Sahwa Ƴan Ƙasar Sudan Da Aka Yaɗa Mutuwarsu Sama Da Shekaru 10 Suna Nan A Raye.

Page Visited: 6713
2 0
Read Time:2 Minute, 18 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Shahararrun makawan yabon annabin nan cikin harshen labaraci yan kasar Sudan da ake kiransu Firkatul Sahawa suna nan da ransu ba kamar yadda aka yadawa cewar sun mutum ba.

VOA Hausa ta rawaito ce wa dan jarida mai zaman kansa a kasar Sudan, Salman al-Parisi, ya fadawa filin “A Bari Ya Huce…” cikin wata hira ta musamman cewar hatsarin mota da ya faru cikin dare ya girgiza hukumomi a Sudan, har ma a lokacin ta haramta yin tafiye-tafiye cikin mota da daddare.

Malam Salman ya ce wadanda suka mutu a wannan hatsari sun hada har da Awad Rashid Ahmad, da al-Ma’sum Umar da kuma Zain al-Abidin al-Sheikh. Daga cikin mawaka hudun da suka yi fice a wannan kungiya ta Firqatul Sahwa, mutum guda ne ya tsira da ransa, At-Tarefi Ahmad, dan’uwan Awad Rashid Ahmad.

To sai dai a wani lamarin ai ban mamaki mawakan sun bayyana da ransu, inda a yanzu haka ma suke wata ziyara a Najeriya.

Alhaji Kawu Habibu Musa, shine wanda ya jagoranci mawakan zuwa Najeriya ya fadawa Expess Radio suna nan da ransu basu mutu ba, inda ya yi karin baniyin kan abinda ya faru da su ake cewa sun mutu.

“Waɗannan bayin Allah dai kamar yadda mutane ke magana kan cewa, mutanen sun mutu to mutane fa basu mutu ba, wallahi da ran su,” in ji Kawu.

“Suna nan da ran su kamar dai yadda kuka gani soyayyarmu da Sayyiussadati ita ce ta sa mukai group da ni da abokai na bayan sun gaya mun wannan maganar sai nayi gaggawa, nace to tinda suma masoya ne irina kuma Ubangiji gashi Allah ya haɗa mu gaba ɗaya, duk dai baki dayanmu muna tare, to yakamata mutanen su zo mana cikin jihar Kano Najeriya dan su wake mana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.”

Kawu ya kuma kara da cewa “su dai waɗannan bayin Allah lokacin da suke wakokin su a ƙasar Sudan suna yin wakokin ne ga Muhammadur Rasulullahi shi kuma shugaban ƙasar Sudan yana so a wake shi a dukkan wakar da za a sa to rashin sa shi da basu yi a wakokin su ba, shine ya jawo matsala.”

“To akwai Sahwa akwai kuma masu irin kwaikwayar su to waɗannan masu kwaikwayon nasu sai suka yi hatsarin mota suka mutu gaba ɗaya su kuma sahawan sai shi shugaban ya ɗebe su ya boye su, sai ya nuna cewa sune suka mutu, duk duniya dai ta shina kwanan aka yi masa juyin mulki, bayan anyi masa juyin mulki, Allah ya karbi mulkin a hannunsa daga baya kuma shugaban da ya hau sai ya sako su,” acewarsa.

Ko a daren ranar Litinin sai da mawakan suka gabatar da majalisin kasidu a gidan kadiriyya Kabara Kano Najeriya.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *