January 31, 2023

Mayan Titunan Jihar Kano Da Gwamnati Ta Haramtawa Masu Adaidata Sahu Bi.

Page Visited: 192
0 1
Read Time:1 Minute, 21 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Gwamnatin jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya  ta haramta wa Ƴan Adaidaita Sahun bin wasu manyan titunan jihar baki ɗaya.

Gwamnatin ta ɗauki matakin ne ta hannun  Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jihar KAROTA.

Sanarwar dokar ya fito ne cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulɗa da jama’a na hukuma KAROTA  Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta ce haramcin zai fara aiki ne a cikin wannan makon a ranar “Laraba 30 ga watan Nuwamba, 2022.”

Samar da motocin daukar fasinja da gwamnatin jihar ta yi ne yasa aka ɗauki matakin “an  ɗauki matakin ne bayan da aka samar da manyan motocin da za su dinga ɗaukar al’umma a titinan da aka haramtawa yan Adaidaita Sahun” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ambato manyan titunan da aka hana masu Adaidaita Sahun ba “an haramta wa direbobin Baburin Adaidaita Sahun bin titinan  Amadu Bello By Munduɓawa zuwa Gazawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo,g “wamnatin ta  tanadi manyan motocin sufuri domin sauƙaƙawa al’umma bin waɗannan hanyoyi.”

Sai dai kuma nan gaba akwai wasu hanyoyin na daban da za a iya ƙara hana bin masu Adaidaita Sahun “gwamnatin za ta sanar da ranar da matuƙa Adaidaita Sahun za su daina bin wasu manyan titinan da zarar gwamnatin ta samar da ababen hawan da al’umma za su yi amfani da su a waɗannan hanyoyi, acewar sanarwar.

A watannin baya ne gwamnatin jihar ta haramtasa Ƴan Adaidaita Sahun aiki a jihar Kano daga karfe goman dare zuwa ƙarfe 6 na safe, al’amarin da gwamnatin jihar ta ce ta yi haka ne saboda dalilan tsaro.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *