Daga Suleman Ibrahim Modibbo
A ranar Alhamis ɗin jiya ne, Gwamnan jihar Gombe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Muhammad Inuwa Yahaya, ya gana da shugaban Kamfanin samar da man fetur na ƙasar Mele Kyari, a Abuja.
Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran Gwamnan Ismaila Uba Misilli, ya fitar a jiya Alhamis wadda ya sanya wa hannu ta ce, “taron wadda aka yi a asirce, ɗori ne kan wasu da dama da Gwamnan ya yi da shugabannin NNPC, a matsayin Gwamnan Jihar Gombe kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, a ƙoƙarinsa na tabbatar da cewa Gombe ta kasance cikin jihohi masu faɗa a ji a harkokin makamashi da tattalin arziƙi a Najeriya.”
Gwamnan Gombe Ya Sa Hannu Kan Takardar Yarjejeniyar Samar Da Tashar Wutar Lantarki A Jihar.
Hukumar Kula Da Shige Da Fice Ta Najeriya Ta Yi Ƙarin Girma Ga Wasu Jami’anta A Jihar Gombe.
Sanarwar ta ce Gwamnan ya kuma yi amfani da damammakin da Jihar Gombe ke da shi a matsayin cibiyar harkokin man fetur da iskar gas a Arewa, musamman duba da ayyukan haƙo mai na Kolmani da sauran harkokin zuba jari da suka shafi makamashi.
“Gwamna Inuwa Yahaya, a ko dabyaushe ya na nuna jajircewa wajen inganta haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki kamar hukumar NNPC da sauran hukumomin ƙasa da na ƙasa da ƙasa don samar da ci gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa ga al’ummar jihar Gombe da Arewa maso Gabas dabma Arewa baki ɗaya”, in ji Ismaila Uba Misilli.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An banka wa gidaje 24 da runbunan ajiyar hatsi wuta a jihar Jigawa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani.
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.