Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Rundunar `Yansandan jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta ce, ta kama wata mai suna Shamsiyya da ta jima ta na nema tawon shekara guda, bayan an zarge ta da aikata laifuka.
Cikin wasu sakwanni da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kakakin Yansandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa, sun kama Shamsiyya da saraurayinta wanda ya ke taimaka mata wajen aikata laifuka, shi ma mai Adaidaita Sahun da ya ke kai ta in da ta ke aikata laifukan ya shiga hannu.
Kiyawa ya kara da cewa, wanda ya ke taimakawa Shamsiyya ta fannin Internet ya shiga hannu, da kuma abokin saurayinta.
Me ya sa PDP ke kallon jawabin Tinubu a matsayin soki-burutsu?
Nan da Makwanni Ƴan Najeriya za su yi murmushi a 2025 – Shettima.
NAHCON ta amince da kamfanoni 10 don jigilar aikin Hajjin 2025.
Wasu laifuka ake zargin Shamasiyya ta aikata har `Yansanda su ka tsare ta?
Da alama dai Shamsiyya dambafarar mutane ta ke yi, in da ta ke bin mata har gida na musu wayo ta karbe musu wayoyin hannu, in da ta ke gudu wa da su.
`Daya daga cikin matan da ta yi wa sata wadda aka sakaya sunanta, ta bayyana wa `Yansanda yadda ta fada komar Shamsiyya “budurwar nan ta je gidana ta ce, za ta siyi Jouk bayan nan sai ta `dauke mun wayata ta tafi da ita, da na kira, ta bukaci na bayar da dubu 100 za ta ban wayar, bayan na tura dubu darin su ka jani har Rijiyar Zaki karshe ba waya ba kudin“.
Ita wata mata da ta ke zargin Shamsiyyar ta sace mata waya har gida ta ce, “wannan Shamsiyya ta zo gidana a ranar 29 ga watan Nuwanba ta ce, ta zo make up, farko ma dai gidan makociyata ta je ta ce dan Allah ta na so a raka ta in da ake yin make up, sai ta hada ta da yarinya ta rakota gidana da ta kawo ta ita sai ta tafi.
“Ta yi ta bani labari, ta ce ai ita ma amarya ce na kawo ta gidan nan, ta nuna mun wani sabon gida, ita Shamsiyyar ta ce amarya ce, ba ai wata daya ba da yin bikin an kawo ta nan kusa da mu, ta ke cewa ai yanzu bikin da za a yi na dangin mijinta ne saboda haka in yi mata kwalliya sosai na fito da ita saboda za ta shiga dangin miji, mu na cikin haka in shiga in yi alwala na yi Sallah na bar wayoyina guda biyu a falo, amma akwai mai aikina a falon, to ita ta tsuguna za ta saka waya chaji, ita kuma shamsiyya ta dauki wayoyina guda biyu da iPhone da Samsung a kan kujera ta fita, daman ta na ta waya ta na cewa za a kawo mata kayanta ne ta na yin kwatancen gidanmu, sai daga baya na gane masu Adaidaita Sahun tare su ke“, in ji wadda aka sace wa wayar ta biyu.
Ba su kadai Shamsiya ta sace wa wayoyi ba, akwai wasu mutum 7 da Kiyawa ya wallafa muryoyinsu in da suke zarginta da sace musu wayoyi a gidaje daban-daban, ya kuwa wallafa cewa, da Safiyar Alhamis bayan sanar da kama ta a ranar Laraba mutane da dama sun je ofishinsu domin shigar da korafinsu a kanta, ta re da karin wasu sama da mutum 20 da su ka kira waya suna korafin suma Shamsiyya ta mamaye su.
Wace ce ita wannan Shamsiyya da ta kware wajen yi wa mutane wayo ta na karbe musu wayoyi?
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani cikakken bayani da `Yansandan su ka bayar kan ko wacece Shamsiyya, da wadanda su ke hada kai wajen aikata laifi, sai dai Kiyawa ya bayyana sunanta da Shamsiyya kuma wadda su ka jima suna nema, abin da ya sa mutane da dama ke dasa ayyar tambaya kan ko wacece Shamsiyya da kuma nuna zakuwa a kafafen sada zumunta wajen ganin an bayyanata ko dora hotonta.
Martaba FM Online, ta yi kokarin ji yo muku ta bakin `Yansandan Kano, kan shin ko wacece Shamsiyya? amma Kakakin Yansandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai amsa kiranmu ba kuma bai dawo mana da amsar sakon karta kwana da mu ka aika masa ba.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamna Zulum zai saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boka Haram ya shafa.
-
Sarakunan da Fintiri ya naɗa bayan ƙirƙirar masarautu 7 a jihar Adamawa.
-
Jami’an tsaro sun ragargaza Lakurawa a jihar Kebbi.
-
Matatar Man Dangote ta ƙulla yarjejeniya da wasu kamfanoni don karya farashin man fetur a Najeriya.
-
Me ya sa PDP ke kallon jawabin Tinubu a matsayin soki-burutsu?