January 5, 2025

Me ya sa PDP ke kallon jawabin Tinubu a matsayin soki-burutsu?

Daga Suleman Ibrahim Modibbo.

Jam’iyyar a Najeriya, PDP ta ce jawabin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa al’ummar kasar na sabuwar shekarar 2025, turanci ne kawai a aka rubuta masa ya karanta, ba abu ba ne na zahiri ba.

Za zantawarsa da BBC tsohon sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa Sanata Umaru Tsauri, ta yi martani da cewa kalaman da Tinubu ya yi soki-burutsu ne kawai.

PDP ta ce duk abubuwan da Tinubun ya fada na cewa gwamnatinsa ta samu nasara, kamata ya yi a ce an gan su a fili muraran, kamar yadda akan ce, ”an ce da kare ana biki a gidanku ya ce to mu gani a kasa.”

Nan da Makwanni Ƴan Najeriya za su yi murmushi a 2025 – Shettima.

Gwamnatin jihar Gombe ta amince da biyan kuɗaɗen giratuti naira Biliyan 4.205

Bankin Duniya ya ce har yanzu Najeriya ba ta kama hanyar yaƙi da rashawa ba.

Tsauri ya ce duk abubuwan da ya fada ba a takarda ya kamata a gan su ba, ya na mai nuni da cewa idan har gaskiya ne gwamnatin ta samu wannan nasara da Tinubun ya fada to jama’a su gani amma lamartin sabanin haka yake.

”Ba abin mamaki ba ne in Shugaban Kasa ya yi waɗannan maganganu domin kawai ya sanar da ƴan Najeriya ba don ya daɗaɗa masu ba, don duk abin da ya faɗi kowa ya sani ba za a ce ƙarya ba ne amma ba gaskiya ba ne – misali in an ce mana farashin mai ya ragu yaushe ya ragu?” In ji shi.

Ya ce gwamnati na cewa farashin dala ya ragu naira ta kara samun daraja, to amma ya yi nuni da cewa, ” mun wayi gari dala ta koma naira 1600 daga naira 1700, cewa ake an samu nasara, to wace nasara aka samu bayan lokacin da Buhari ya hau mulki muna sayen dala naira tamanin?”

”To wane irin cigaba ne wannan? Mu a wurinmu Turanci ne aka rubuta kuma ya karantu,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *