Musayar yawu da ke ci gaba tsakanin Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ta ɗauki sabon salo a ranar Asabar, yayin da mijinta Cif Emmanuel Uduaghan ya buƙaci Akpabio da ya girmama matar sa tare da ba ta martaba da daraja da ta cancanta da ita.
Uduaghan wanda shi ne Aleman Masarautar Warri, a wata sanarwa da ya fitar a Warri Jihar Delta, ya bayyana cewa tun da farko ya ƙi yin tsokaci kan rikicin, amma ya ga ya zama dole ya yi magana sakamakon abubuwan da ke faruwa kwanan nan.
Ya nuna damuwa kan yadda lamarin ke ƙara tada hankali, ya na mai cewa hakan na kau da hankali daga muhimman batutuwan da suka dace a mayar da hankali a kansu.
Ya ce “Ba tare da la’akari da shari’ar da ke gudana ba, ina so in jaddada cewa matata ta samu nasarar zama sanata ne bisa soyayya, girmamawa, da amana da mutanenta ke da ita gare ta.
Ya kara da cewa “Ta sadaukar da kanta wajen kawo wakilci mai inganci ga yankinta da ƙasa baki ɗaya.”
Uduaghan ya bayyana Natasha a matsayin mace mai rikon amana da gaskiya, duk da wahalhalun da take fuskanta.
Ya bayyana cewa ta gaya masa game da mu’amalar ta da Shugaban Majalisar Dattawa, wanda shi ma yake ɗauka a matsayin abokin arziki ga iyalin su.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
PDP ta sake dage taron Kwamitin Zartaswar ta na Kasa (NEC) zuwa ranar 15 ga watan Mayu.
-
Tinubu ya ya tabbatar da cewa tattalin arziƙin Najeriya ya na farfaɗo wa.
-
Ba zan yi musayar yawu da El-Rufai ba,-Ribadu
-
“Dubban mutane na shigowa jam’iyyar mu, ba da daɗewa ba, za mu karɓi manyan jiga-jigan NNPP da kansu”-Ganduje
-
Ƴan jam’iyyar APC sama da dubu 7 sun fice daga jam’iyyar zuwa PDP a jihar Bauchi.